An Bude Taron Shekara-Shekara Na Dandalin Tattauna Raya Kasa Na Sin Na 2025
Published: 24th, March 2025 GMT
A yau Lahadi ne aka bude taron shekara-shekara na dandalin tattauna raya kasa na kasar Sin na 2025 a nan birnin Beijing, taron da cibiyar binciken raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta shirya tare da hadin gwiwar asusun binciken raya kasa na kasar Sin. Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci bikin bude taron, inda ya gabatar da muhimmin jawabi, wanda a cikinsa ya jaddada aniyar kasar Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje.
Shi ma mataimakin darektan ofishin kula da harkokin yau da kullum na hukumar kudi da tattalin arziki ta kwamitin kolin JKS Han Wenxiu, wanda ya halarci taron na shekara-shekara, ya ce kasar Sin za ta dauki dukkan matakai na habaka kashe kudi, da kuma ci gaba da haifar da yanayi, ta yadda ingantaccen ci gaba da kyakkyawar rayuwa za su rika karfafar juna.
Hajiya Safara’u, Mahaifiyar Gwamna Raɗɗa Ta Rasu An Kashe Askarawa 6 da ‘Yan Sa-kai 4 A ZamfaraZa a shafe kwanaki biyu ana gudanar da taron, bisa jigon “Ingiza karfin ci gaba, tare da inganta kyakkyawan ci gaban tattalin arzikin duniya”. Taron ya hallara wakilai daga manyan kamfanoni 86 na kasashe 21. A yayin taron, mahalarta na kasar Sin da na kasashen waje, za su gudanar da tarukan karawa juna sani 12, kan batutuwan da suka hada da manyan manufofi, da yin gyare-gyare, da kara yawan amfani da kayayyaki, da sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da fasahar AI.
Tun lokacin da aka kaddamar da dandalin tattauna raya kasa na kasar Sin a shekarar 2000, dandalin ya zama wata muhimmiyar gada da ta sa kaimi ga yaukaka tattaunawa, da hadin gwiwa tsakanin Sin da sauran kasashen duniya. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: raya kasa na na kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da hajojin masana’antu na kasa da kasa.
Kakakin ya kara da cewa, kasashen duniya suna maraba da hajojin kasar Sin, kuma yakin ciniki da haraji ba su yi wani babban tasiri kan kasar Sin ba. A fannin hada-hadar cinikayya, sanya shinge ba alama ce ta karfin gwiwa ba, kuma katangar da Amurka ke ginawa kanta, daga karshe za ta illata karfinta ne.
Lin Jian, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau Laraba, ya ce yayin da ake fama da yanayi mai sarkakiya, da sauye-sauye masu maimaituwa daga ketare, cinikayyar waje ta Sin na gudana lami lafiya, cike da karfin juriya da babban karsashi.
Hakan a cewarsa, ya shaida gazawar yakin haraji da cinikayya wajen girgiza fifikon da Sin ke da shi, a fannin raya masana’antun sarrafa hajoji da kasar ta gina a tsawon lokaci. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp