Biza: UAE ta ƙaƙaba wa ’yan Najeriya sabbin takunkumai
Published: 9th, July 2025 GMT
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), ta ƙara sanya wa ’yan Najeriya da ke son ziyartar Dubai sabbin sharuɗa.
Haka kuma, ta dakatar da bayar da bizar wucin gadi ga ’yan Najeriya.
Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – MinistaAminiya ta samu labarin cewa hukumomin shige da fice na Dubai ne suka bayar da umarnin sabbin matakan ga ofishin jakadancin ƙasar da ke Najeriya.
Daga cikin sabbin dokokin, duk ɗan Najeriyar da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 45 ba zai samu bizar yawon buɗe ido ba sai idan zai yi tafiya tare da wani.
Wannan na nufin cewa yawan ’yan Najeriya da ke tafiya Dubai zai ragu, duba da yadda birnin ke da farin jini wajen kasuwanci da yawon buɗe ido.
A bara UAE, ta janye haramcin biza da ta sanya wa ’yan Najeriya na tsawon shekaru biyu.
Amma janye haramcin ya zo ne da sharuɗa masu tsauri, kuma yanzu ta ƙara tsaurara su.
Wani muhimmin canji a cikin sabbin ƙa’idojin shi ne cewa ba za a ƙara neman bizar wucewa ba daga ’yan Najeriya.
Sannan duk wanda ya haura shekaru 45, sai ya gabatar da bayanin asusun bankinsa na tsawon watanni shida da suka gabata.
Kuma kowane wata dole ne asusun ya zamana akwai aƙalla dala 10,000 ko dai daidai da hakan a kuɗin Naira.
Ƙasar ta ce dole ne a cika waɗannan sharuɗan tare da sauran takardun da ake buƙata da bayanan fasfo.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya Sharuɗa yan Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a.
Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki da kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su samu nasara a rayuwarsu.
Gwamna Uba Sani, ya kuma halarci shirin baje koli na birnin Dubai mai taken : “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira, da Tasirin Zamantakewa”, inda nan ma ya jaddada cewa jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha a mulki suna da matuƙar muhimmanci wajen buɗe damarmaki ga mutane da birane.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da wata ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta Janar na birnin Dubai inda suka tattauna batutuwan haɗin gwiwa a fannin kirkirar makamashin sharar gida da kula da sharar gida ta zamani, da kuma tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
A ganawar, duk Bangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin jihar Kaduna zuwa tattalin arzikin mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Jihar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun ƙasashen duniya wajen yin haɗin kai, ƙirƙira, da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa da ci gaban kowa da kowa a fadin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA