Hukumar EFCC Ta Kai Wa Yaran Makaranta Yaki Da Rashawa A Ilorin
Published: 9th, July 2025 GMT
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Ilorin ta kai wa daliban makaranta yakin da ta yi da cin hanci da rashawa domin fadakar da su illar cin hanci da rashawa.
Da yake jawabi ga dalibai a makarantar Nursery da Primary School, Tanke, Ilorin, Shugaban Sashen Hulda da Jama’a, Daraktan Hukumar EFCC, Ayodele Babatunde, ya ilmantar da daliban a kan ma’anar cin hanci da rashawa, daban-daban da illolinsa da yadda kowa da kowa, ciki har da yara, za su iya bayar da tasu gudunmuwar wajen gina Nijeriya mara cin hanci da rashawa.
Ya ce cin hanci da rashawa yana yin abin da bai dace ba ne, musamman idan ya shafi wasu ko kasar da suka hada da munanan dabi’u kamar ha’inci da karya da kuma sata.
Babatunde ya ce yara suna da rawar da za su taka wajen samar da makoma mai kyau ko da a kanana.
“Za ku iya kauce wa cin hanci da rashawa ta hanyar fadin gaskiya a kodayaushe, yin aikin gida ba tare da yin kwafin wasu ba, kin yin sata ko zamba, kiyaye gaskiya, da’a, amana, da kishin kasa da mutunta doka a gida da makaranta,” inji shi.
Babatunde ya kara karfafa gwiwar daliban da su tabbatar sun girma a matsayin ’yan kasa nagari masu kaunar kasarsu tare da yin watsi da ayyukan da ka iya cutar da ci gabanta.
Tattaunawar ta kunshi tambayoyi daga daliban da kuma alkawarin zama jakadun yaki da cin hanci da rashawa a makarantarsu da gidajensu.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU/Ilorin
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: cin hanci da rashawa
এছাড়াও পড়ুন:
Masanin Kenya: Kasashe Masu Tasowa Suna Bukatar Kasar Sin
Masanin Kenya kan huldar kasa da kasa mai suna Cavince Adhere, ya bayyana a yayin zantawarsa da dan jarida na kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa ya jaddada daidaito da samun albarkatu, inda hakan ya samu aminci daga kasashe masu tasowa. Kuma har ila yau, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashe masu tasowa ya riga ya samu gagarumin ci gaba, don haka makomar kasashe masu tasowa na bukatar ci gaba da kasancewar Sin a cikinsu.
Bugu da kari, Cavince Adhere ya jaddada cewa, Sin ta bayyana bukatun kasashe masu tasowa na duniya yadda ya kamata, kana tana inganta ra’ayoyin da suka dace da muradunsu, kamar yadda aka samu ci gaba da kuma bunkasa a tsarin BRICS. Cavince Adhere ya ce, “Ta hanyar kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa, da yin mu’amala da juna a fannin al’adu, da bullo da sabbin ra’ayoyi a fannonin raya kasa da kasa, Sin ta zama wani muhimmin karfi wajen gina tsarin dunkulewar kasa da kasa.”
Kazalika, ya ce, “Ko shakka babu, kasashe masu tasowa ma za su kasance wani karfi wajen inganta ci gaba mai dorewa a karni na 21.”(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp