’Yan ƙabilar Ibo ne suka fi aikata laifi a Jihar Anambra ba Fulani ba — Gwamna Soludo
Published: 10th, July 2025 GMT
Gwamana Charles Soludo na Jihar Anambra ya ce mafi rinjayen kaso na waɗanda jami’an tsaro ke kamawa da aikata laifuka tsawon shekara uku da suka gabata ’yan kabilar Ibo ne.
BBC ya ruwaito Soludo yana bayyana hakan a yayin wani taro da ’yan asalin jihar mazauna ƙetare suka gudanar a Amurka.
Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyyaSoludo wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne ya yi watsi da zargin da ake yi wa Fulani makiyaya na aikata satar mutane a jihar.
“Yanzu shekara uku da wata uku ke nan ina kan mulki. Idan muka kama masu laifi 100 to kashi 99 cikin 100 matasan ƙabilar Ibo ne,” a cewar gwamnan.
“Karya da farfaganda ake yaɗawa cewa Fulani ne ke aikata laifukan. Waɗannan karerayin da ake yaɗawa su suka buɗe kofa ga matasanmu shiga satar mutane saboda ta fi kawo kuɗi kan sana’arsu ta ‘Yahoo’ da safarar ƙwayoyi.”
Anambra na cikin jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya da ’yan bindiga masu fafutikar kafa ƙasar Biafra suka dinga hana mutane fita harkokinsu duk ranar Litinin a baya domin nuna ɓacin ransu kan kamawa da kuma tsare jagoransu Nnamdi Kanu da Gwamnatin Tarayya ta yi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Farfesa Charles Soludo jihar Anambra
এছাড়াও পড়ুন:
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe.
Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta walwalar malamai.
Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyiYa ce: “Ba za mu taɓa barin malamai su shiga cikin matsanancin hali ba. Za mu duba matsalolinsu domin tabbatar da walwalarsu da ci gaban ilimi a jihar.”
Sani, ya kuma yaba da yadda NUT ke tattaunawa cikin lumana da kawo shawarwari maimakon ɗaukar matakan da za su iya kawo tsaiko ga harkar ilimi.
A nasa jawabin, shugaban NUT na jihar ya ce sun kai ziyarar ne domin tattauna matsalolin da malamai ke fuskanta, musamman na makarantun firamare da ƙananun sakandare da ke ƙarƙashin kulawar ƙananan hukumomi.
Ya ƙara da cewa manufar NUT ita ce samar da fahimtar juna da haɗin kai tsakaninsu da shugabannin ƙananan hukumomi domin gano hanyoyin magance matsaloli cikin lumana.