Aminiya:
2025-07-31@17:39:35 GMT

Yadda garin Zip ya nutse a Kogin Binuwai

Published: 23rd, March 2025 GMT

Wani abin al’ajabi da ban tsoro ya auku inda rana tsaka garin Zip da ke Jihar Taraba ya nutse baki dayansa a cikin Kogin Biniwai.

Wakilin Aminiya ya ziyarci garin domin gani da ido, inda ya ruwaito cewa a halin yanzu babu sauran wani gini ko bishiya da ake gani a garin, duk kogin ya hadiye su, sun nutse a cikin ruwa.

Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu

Garin na Zip da ke Karamar Hukumar Karim-Lamido ta Jihar Taraba yana bakin Kogin Biniwai ne, kuma mafi yawan mazaunansa masunta ne da manoma.

Sun kuma bayyana wa wakilinmu yadda abin ya faru da yadda suka tsallake rijiya da baya da irin asarar da suka tafka da kuma halin da ibtila’in ya jefa su a halin yanzu.

Wani mazaunin garin, Alhaji Gambo Sa’idu, wanda kuma dan uwan sarkin garin ne, ya shaida wa wakilinmu cewa, a gidansa akwai dakuna fiye da takwas kuma gidan nasa kamar sauran gidajen garin duk sun nutse a cikin Kogin Biniwai.

Yadda abin ya faru

Ya kara da cewa tun a shekarun baya ne al’ummar garin suka fara ganin gine-ginen da suke bakin gabar kogin garin sun fara tsagewa, daga bisani wasu suka fara ruftawa suna fadawa cikin kwaryar kogi.

Alhaji Gambo ya ce, “Tsohon Sarkin Zip, Marigayi Alhaji Uba Sa’idu ya kai rahoto ga Karamar Hukumar Karim-Lamido da kuma Gwamnatin Jihar Taraba kan yadda gidaje ke ruftawa suna ta fadawa cikin ruwa, amma babu wanda ya zo ya duba abin dake faruwa.”

Kwatsam ƙasa ta fara motsi gidaje na ruftawa

“A cikin daminar da ta wuce ne kawai al’ummar garin suka ga wasu sassan garin na motsi sai kuma gine-gine suka fara darewa.

“Da muka ga kasa tana motsi gine-gine kuma suna darewa sai muka shiga kwashe iyalanmu da kayayyakinmu daga cikin gidajenmu domin gudun kada gidajen su rufta cikin ruwa da iyalanmu da kayayyakinmu.

“A cikin wannan yanayin gine-gine da suke cikin garin dukkansu suka rufta cikin ruwa kuma ruwa da yashi suka rufe garin baki daya,’’ in ji shi.

Ruwa ya haɗiye gine-gine

Ya ci gaba da cewa “In ba wanda ya san dama akwai gari a wajen ba, babu wanda zai taɓa cewa akwai gari a can baya kafin wannan lamari ya faru, ba za a taba cewa akwai gari a nan ba.

“Ga inda garin Zip yake can ruwa da yashi sun rufe shi, abu daya ne ake gani, shi ne rodin da aka yi amfani da su wajen gina masallacin Juma’a, su ne kadai ba su nutse a cikin yashi baki daya ba,’’ in ji Gambo.

Gidana ta nutse a ruwa – Malam Bashiru

Malam Bashiru Gambo shi ma mazaunin garin na Zip ne, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa ya kashe kudi kimanin Naira miliyan bakwai wajen gina gidansa mai dakuna shida a lokacin da kayan gini ke da arha.

Ya ce gidan nasa dungurumgum ya nutse a ruwa, amma dai Allah Ya taimake shi iyalinsa sun tsira, in banda wasu kayayyakinsa da suka nutse a ruwa.

A cewarsa, idan zai sake gina gida kamar nasa a yanzu, to zai kashe kudi fiye da Naira miliyan goma sha biyar saboda tsadar kayan gini.

Iyalai sun koma zama a bukkoki

Magidancin ya ce yanzu shi da iyalinsa da sauran mutanen sun koma zama a cikin bukkoki da suka yi na ciyawa saboda ba su da kudin da za su sake gina wasu gidaje.

Malam Bashiru ya ce, “Masallacin Juma’a da makarantar firamare da asibiti da kuma coci kamar sauran ginegine da ke garin duk sun rufta a cikin ruwa.

“Yanzu masallacin Juma’a da ciyawa aka yi shi, sa’annan kuma yaranmu ba sa zuwa makaranta domin har yanzu ba a sake gina wata makaranta a garin ba, kuma mata masu juna biyu da kananan yara ba sa samun kula ta fuskar kiwon tafiya.

“Abin mamaki shi ne yanzu ba wani taimako da mu al’ummar wannan gari muka samu daga Gwamnatin Jihar Taraba kuma yanzu ga shi lokacin damina na kara gabatowa,’’in ji Bashiru.

Mijina ya kamu da rashin lafiya – Hussaina

Wata matar aure mai ’ya’ya takwas mai suna Malama Hussaina Muhammed ta shaida wa wakilin Aminiya cewa da kyar ta tsira tare da mijinta da ’ya’yanta a lokacin da garin ya nutse a ruwa.

Ta ce duk da cewa sun tsira, amma a sanadiyyar wannan matsalar mijin nata, Malam Muhammed ya sami rashin lafiya, wanda a yanzu haka ya bar garin Zip ya koma wani gari ya bar ta da ’ya’yanta suna zaune a ’yan bukoki.

Malama Hussaina ta ce katifunsu da wasu kayayyaki duk sun nutse a ruwa kuma tana cikin halin kaka-ni-ka-yi domin mjiiin nata ya bar ta ita kadai kuma ’ya’yan nata kanana ne.

Kamar girgizar kasa

Shi ma Malam Ya’u Baba Tsoho, ya ce ba su taba fuskantar irin wannan ibtila’in ba, duk da kasancewar garin na Zip ya dade.

Ya ce, “Za a iya danganta hatsarin da ya auku a garin da cewa girgizar kasa ce domin a ranar da lamarin ya faru, garin ya motsa kuma gine-gine suka dare kuma dukkan gidajen suka yi ta ruftawa cikin kogi har da bishiyoyi ma da ke ciki da kewayen garin na Zip, duk sun nutse a cikin ruwa.”

Babu dauki daga gwamnati

Ya ce, “A can baya lokacin da jama’ar garin suka ga ginegine na tsagewa sarkin garin, Marigayi Uba Sa’idu ya kai rahoto ga Karamar Hukumar Karim-Lamido da kuma Gwamnatin Jihar Taraba har ma da hotuna, amma babu abin da hukumomin Jihar Taraba suka yi har ya zuwa lokacin da garin baki daya ya rufta a cikin ruwa.

“Har zuwa yanzu babu wani jami’in gwamnatin Jihar Taraba ko kuma na Karamar Hukumar Karim-Lamido wanda ya ziyarci garin domin ganin abin da ya faru, kai ma da kanka ka ga inda tsohon garin yake, ruwa da yashi sun rufe garin baki daya, ba wani alamar gini ko bishiya, kuma a yanzu duk al’ummar garinmu a bukoki muke zaune,’’ in ji Ya’u.

Mista Micah Dantala lsoko, wanda shi ne Magatakardan Sarkin Zip, ya shaida wa Aminiya cewa duk gine-ginen da ke garin sun nutse a cikin ruwa wanda haka ya haifar wa da jama’ar garin asarar dukiya mai yawan gaske.

Ya bayyana cewa Masallacin Juma’a da coci da makarantan firamare da asibiti suna daga cikin gine-ginen da suka nutse baki daya a cikin kogin na Biniwai.

Ya ce har yanzu babu wani dauki da aka kawo wa jama’ar garin don a tsusayawa.

“Mun yi sa’a ba a samu asarar rai a laokacin wannan hadari ba, amma daukacin gine-ginenmu da kayayyakimu duk sun nutse a cikin ruwa yanzu kusan duk al’umma suna zaune tare da iyalansu a dakunan ciyawa domin kayan gini sun yi tsada sosai,’’ in ji Micah.

Shi ma Sarkin garin na Zip, Malam Yusuf Babatato, ya bayyana cewa al’ummar garin sun yi asarar daukacin gidajensu da wuraren kasuwanci da masallatai da coci da makarantar firamare da asibiti.

Ya ce, “Kamar yadda duk wanda ya zo nan zai gani, kusan dukkan jama’a dakunan ciyawa suke zaune tare da iyalinsu.”

Shirin gina sabon gari ya samu cikas

Malam Yusuf Babatato, ya ce a halin yanzu sun sami wani wuri nesa da tsohon garin da ya nutse a ruwa za su gina sabon gari, amma matsalar kudi ta kawo jinkiri wajen fara aikin.

Ya ce, “Babbar matsalar da ke damun al’ummar garin ita ce rashin makaranta da asibiti domin sai an tafi wurare masu nisa ake samun kulawa ta fuskar kiwon lafiya, yara kuma suna zaune ba sa zuwa makaranta domin har yanzu ba a sake gina wata makaranta ko asibiti a garin ba.”

Duk kokarin da wakilin Aminiya ya yi domin jin ta bakin Kwamishinar Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Taraba, Hajiya A’isha Barde, ya ci tura domin ba ta amsa kiran waya ba.

Wakilin namu ya tura mata rubutaccen sakon waya, inda ta dawo masa da amsar cewa ba ta sami labarin abin da ya auku a garin na Zip ba. Sai dai kuma ba ta yi wani bayani game da ko akwai wani mataki da gwamnatin Jihar Taraba za ta dauka kan lamarin ba, har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoton.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Binuwai Jihar Taraba Karamar Hukumar Karim Lamido sun nutse a cikin ruwa al ummar garin nutse a ruwa garin na Zip Jihar Taraba

এছাড়াও পড়ুন:

2027: Ba Mu Kafa Haɗakarmu Don Cika Burin Atiku Ba – ADC

Abdullahi ya ce tun kafin a kafa haɗakar, wasu sun riga sun fara yaɗa cewa an shirya ta ne domin Atiku.

Ya ƙara da cewa: “Ni ina da shekara 56, wa ya ce ba zan iya tsayawa takarar shugaban ƙasa ba?”

Da aka tambaye shi game da Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Abdullahi ya ce Obi na cikin haɗakar har yanzu.

Amma ya ce bai zama cikakken ɗan jam’iyyar ADC ba har yanzu.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ta bai wa Obi da kuma tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, dama su fice daga jam’iyyunsu na yanzu wato LP da SDP.

Ya kuma ce Obi ba zai koma jam’iyyar PDP ba, duk da cewa jam’iyyar tana ƙoƙarin jawo ‘yan siyasa domin dawo da ƙarfinta.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ‘yan Nijeriya za su yadda da jam’iyyarsu, Abdullahi ya ce jam’iyyar APC da ke mulki ta yi alƙawarin kawo sauyi amma ta gaza.

Don haka, ya ce lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su gwada wata sabuwar tafiyar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
  • 2027: Ba Mu Kafa Haɗakarmu Don Cika Burin Atiku Ba – ADC
  • Gine-gine 8 Sun Ruguje, Makabarta Ta Nutse A Wata Sabuwar Ambaliyar Ruwa A Borno
  • Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • An Fitar Da Kudaden Farfado Da Sassan Birnin Beijing Da Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa
  •  Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
  • Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza
  • Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa
  • Mutanen Sweida Na Kasar Siriya Suna Fama da Rashin Abinci da Ruwa