Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba don haka ‘yan gwagwarmaya ne zasu gindaya sharudda

Izzat al-Rishq mamba a ofishin yada labarai na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Kalaman fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu na sakin dukkan fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya da kuma mika wuyar Hamas sun sabawa matakin hankali da hakikanin abin da ke gudana a fagen yaki.

Al-Rashq ya tabbatar a cikin wani takaitaccen bayani a shafinsa na Telegram da sanyin safiyar Larabar nan cewa: Bayan da shugabannin ‘yan mamaya makiya suka amince da gazawar da suka yi wajen kwato fursunoninsu ta hanyar karfin soja; Ya bayyana cewa babu yadda za a yi a sake su sai ta hanyar sharuddan da ‘yan gwagwarmaya suka gindaya.

Ya jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu gindaya sharudda, kamar yadda ta sanya ma’aunin da ya dace abi.

Kafofin yada labarai sun ambato Netanyahu yana fadar haka daga Washington cewa: Dole ne Gaza ta samu wata makoma ta daban, kuma har yanzu dole ne su kammala aikin sakin dukkan fursunoni tare da kawar da karfin soji da na gwamnatin Hamas gaba daya.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: yan gwagwarmaya

এছাড়াও পড়ুন:

Falasdinawa 13 Ne Suka Yi Shahada Wasu Da Dama Suka Jikkata A Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza

Falasdinawa 13 ne suka yi shahada da suka hada da yara kanana da mata a hare-haren bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan gidaje da matsugunan Falasdinawa a Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza da asubahin ranar Talata, inda suka kai hare-hare kan gidajen fararen hula da matsugunan ‘yan gudun hijira. Hare-haren sun yi sanadiyyar shahadan  fararen hula 13 da suka hada da yara da mata, yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu munanan hare-hare ta sama da aka kai a yankuna daban-daban na zirin.

Asibitin Al-Shifa ya sanar da shahadan Falasdinawa hudu ciki har da wani jariri, sakamakon harin da jiragen yakin sojin mamayar Isra’ila suka kai a wani gida da ke kusa da kasuwar Carrefour a unguwar Tel al-Hawa da ke kudu maso yammacin birnin Gaza. A halin da ake ciki kuma, asibitin Baptist ya sanar da shahadan Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu sakamakon harin da aka kai a gidan Khader al-Jamasi da ke kusa da masallacin al-Ibki da ke unguwar al-Tuffah da ke gabashin birnin.

Wata majiyar lafiya a asibitin Al-Awda da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat ta bayyana cewa: Hari ya jikkata wasu fararen hula a lokacin da makarantar Abu Helu al-Sharqiya da ke dauke da ‘yan gudun hijira a sansanin ‘yan gudun hijira na al-Bureij da ke tsakiyar zirin Gaza ta fuskanci hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ta kai kai tsaye, lamarin da ya haifar da firgici ga iyalan da suka rasa muhallansu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Yemen Ta Bayyana ‘Yancin Kowa Na Walwala A Teku Amma Ban Da ‘Yan Sahayoniyya Azzalumai
  • Hizbullah Ta Kasar Lebanon Ta Godewa JMI Dangane Da Tallafawa Kungiyar Saboda Gwagwarmaya Da HKI
  • HKI Ta Kashe Falasdianwa 6 A Gaza, Kuma Tsoffin Fursinoni
  • ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Halaka Sojojin Mamaya Biyar Tare Da Jikkata Wasu Goma Na Daban
  • Falasdinawa 13 Ne Suka Yi Shahada Wasu Da Dama Suka Jikkata A Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza
  • Reuters: Amurka Tana Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
  • Araqchi Ya Gana Da Babban Malamin Yahudawa Mai Adawa Da ‘Yan Sahayoniyya A Gefen Taron Kungiyar BRICS
  • Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Mamayar Isra’ila Kan Kasar Yemen
  • Falasdinawa Kimani 635 Amurka da HKI Suka Kashe A Cibiyoyin Karban Abinci A Gaza