Hukumar Kiyaye Hadura Ta Kasa Za Ta Aiki Da ‘Yan Jarida A Kano
Published: 9th, July 2025 GMT
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano, ta bayyana kudurinta na kara zurfafa dangantakarta da kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ reshen jihar Kano.
Wannan alkawari ya fito ne daga bakin kwamandan sashin, Kwamandan Corps Muhammad Bature, a lokacin da yake karbar sabbin shugabannin majalisar a hedikwatar hukumar FRSC da ke Kano.
Sabbin shugabannin kungiyar masu aiko da rahotanni ta NUJ sun ziyarci hukumar FRSC ta Kano domin taya rundunar murna kan kokarin da take yi na inganta hanyoyin kiyaye hadurra da kuma gano sabbin hanyoyin hadin gwiwa.
Kwamandan sashin ya yi maraba da ziyarar, inda ya bayyana ta a matsayin wata babbar alama ta tabbatar da ci gaba da hadin gwiwa tsakanin FRSC da NUJ.
Ya bayyana jin dadinsa na yin aiki kafada da kafada da NUJ domin inganta moriyar juna.
Kwamandan sashin ya kuma gayyaci mambobin Kungiyar da su shiga rundunar FRSC Special Marshal Corps a matsayin masu aikin sa kai. Wannan shiri na da nufin tallafa wa kokarin da hukumar ta ke yi a fadin kasar na rage hadurran ababen hawa da asarar rayuka.
Da yake mayar da martani ga kwamandan sashin, zababben shugaban kungiyar ta Chapel, Murtala Adewale, ya ce makasudin ziyarar shi ne don kara tabbatar da alakar da ke tsakanin FRSC da jami’an kungiyar.
Adewale ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa FRSC zai bayar da dandali fadakarwa da zai kara wayar da kan jama’a kan kiyaye hanyoyin mota a fadin Kano da ma wajen.
Abdullahi Jalaluddeen Kano
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Fursunoni 58 Na Rubuta Jarabawar NECO A Kano
Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana cewa Fursunoni 58 suna rubuta Jarrabawar Kammala Sakandare ta Kasa NECO ta shekarar 2025.
Wannan ci gaba ya samu ne bayan biyan kudin rajista da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Kofar-Nasarawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kano.
Ya ce wannan karamci na gwamnatin jihar Kano shaida ce ta jajircewarta wajen kula da walwalar fursunoni, gyaran dabi’unsu da kuma dawo da su cikin al’umma yadda ya kamata.
“Biyan kudin rajistar jarrabawa da gwamnatin Kano ta yi alama ce ta jajircewarta wajen samar da dama ga fursunoni domin su gyara rayuwarsu su koma cikin al’umma,” in ji shi.
Hukumar ta bayyana godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayansa da hadin kai da yake bayarwa ba kakkautawa.
Ya ce wannan mataki zai karfafa gwiwar fursunoni wajen daukar karatu da muhimmanci tare da ba su wata sabuwar dama ta samun ilimi da kyakkyawar makoma.
Musbahu Kofar-Nasarawa ya kara da cewa, hukumar gyaran hali ta Kano ta kuduri aniyar samar da kyakkyawan yanayi domin gyaran hali da ilimantar da fursunoni.
“Muna alfahari da samun goyon bayan gwamnatin Kano a wannan kokari,” in ji sanarwar.
Ya kuma ce jajircewar hukumar wajen gyaran hali na bayyana ta hanyoyin da take bi wajen samar wa da fursunoni damar samun ilimi da sauran damammaki da za su taimaka musu su gyara rayuwarsu su koma cikin al’umma.
Abdullahi Jalaluddeen