Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Amince Iran ta Kai Hare-Hare Kan cibiyoyin Sojojinta Guda Biyar
Published: 9th, July 2025 GMT
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi furuci da cewa Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin sojojinta
Wani jami’in sojan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci a ranar Talata cewa; Hare-haren da Iran ta kai a watan da ya gabata sun afkawa wuraren sojojin mamayar Isra’ila, matakin da tuni duniya ta amince da kai irin wadannan hare-hare kan cibiyoyin sojin mamaya.
Jami’in da ke magana da kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ki bayar da karin bayani, ciki har da gano wuraren da abin ya shafa ko kuma irin barnar da harin ya yi ga kayayyakin aikin soja.
Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki kan haramtacciyar kasar Isra’ila a watan da ya gabata a matsayin mayar da martani ga hare-haren ba-zata da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a ranar 13 ga watan Yuni kan Iran wanda harin ya auna fitattun shugabannin sojoji da masana kimiyyar makamashin nukiliyar Iran.
Harin na Iran ya sha mai da hankali kan birnin Tel Aviv da Haifa, matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida musamman wuraren da suke dauke da mutane masu yawa da kuma yankin kudancin Falasdinu da aka mamaye kusa da Beersheba, inda ake da cibiyoyin soji.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: haramtacciyar kasar Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yace Mutanen Kasarsa Suna Cikin Shiri Don Kare Kansu Da Karfi
Ministan harkokin wajen kasar Aran Abbas arachi ya bayyana cewa mutanen kasarsa a shirin suke su ci gaba da kare kasarsu daga Amurka da kuma HKI .
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda yake ganawa da tawagar kasar Brazil a gefen taron kungiyar BRICS karo 17 wanda ke tafiya a halin yanzu a birnin Rio de Jenero na kasar Brazil.
An gudanar da wannan taron ne saboda hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa JMI a baya bayan nan, da kuma tasirinsa a cikin al-amuran siyasa da kuma tattalin arziki a yankin Asiya ta yamma da kuma duniya gaba daya.
Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren HKI da kuma Amurka ya sabawa dikokin kasa da kasa sannan ko wane bangare yana da rawar da zai take don ganin an tabbatar da zaman lafiya a duniya.
A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yace: hare-hare kan kasar Iran musamman a kan shirinta na makamashin nukliya na zaman lafiya abin yin tir da shi ne. Sannan ya kara da cewa kasar Rasha a shirye take ta taimaka ko a fagen kwamitin tsaro na MDD ne.