Kasar Yemen Ta Bayyana ‘Yancin Kowa Na Walwala A Teku Amma Ban Da ‘Yan Sahayoniyya Azzalumai
Published: 9th, July 2025 GMT
Shugaban Majalisar Kolin siyasar kasar Yemen ya jaddada ‘yancin kowa da kowa wajen gudanar da zirga-zirga a teku in banda makiya ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu
Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen, Field Marshal Mahdi al-Mashat, ya jaddada aniyar kasar ta Yemen na ba da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa ga kowa da kowa in banda makiya yahudawan sahayoniyya da kuma masu goya musu baya a lokacin da suke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza.
A cikin wata sanarwa da Al-Mashat ya fitar ya ce: Ba su da wani sha’awar kai hari ga duk wanda ba shi da alaka da goyon bayan makiya yahudawan sahayoniyya, yana mai kira ga dukkanin kamfanonin jiragen ruwa da su mutunta umarni da shawarwarin sojojin Yemen, kuma duk wanda ya yi watsi da shawarar zai dauki nauyi abin da zai biyo baya.
Ya kara da cewa: Sun kafa wata cibiyar gudanar da ayyukan jin kai da za ta hada kai da kamfanonin sufurin jiragen ruwa, domin kauce wa illa sosai.
Al-Mashat ya shawarci kowa da kowa da ya guji yin mu’amala da makiya yahudawan sahayoniyya, yana mai jaddada cewa: Dakarun Yemen masu girma da kuma da’a za su ci gaba da gudanar da ayyukansu da nufin kawo karshen hare-haren da ake kaiwa Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kasar Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren HKI Kan Kasar Yemen
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’el Baka’e ya yi allawadai da hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wasu yankuna a kasar Yemen a ranar Lahadi.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya litinin ya kuma yi tir da hare-hare kan a Hudaydah, Ras-Isa, as-Salif da kuma tashar wutan lantarki na Ras al-Kathib.
Har’ila yau Baka’ee ya yi allawadai da kai hare-hare kan cibiyar tattalin arziki na kasar ta Yemen a Hudaida, wadanda suka hada da kayakin jama’a wadanda suka hada da gadoji da hanyoyiu da tashar Jiragen sama, da tashar jiragen ruwa da kuma rumbunan ajiyar abinci. Wandanda gaba dayansu yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Hare-harin ranar Lahadi dai sune na farko bayan kimani wata guda, sannan sun zo ne bayan da yahudawan suke ce wai sun kakkabo dukkan makamai masu linzami wadanda sojojin kasar Yemen suke kaiwa kan HKI.