Iran Ta Musanta Neman Ci Gaba Da Gudanar Da Tattaunawa Da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
Published: 9th, July 2025 GMT
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta sanar da cewa: Iran ba ta gabatar da wata bukatu na ganawa ga bangaren Amurka ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya musanta kalaman shugaban Amurka dangane da muradin Iran na gudanar da tattaunawa, yana mai jaddada cewa: A bangaren Iran ba a gabatar da wata bukata ta yin wata ganawa da bangaren Amurka ba.
Da yake mayar da martani ga kalaman Donald Trump, Ismail Baqa’i ya ce: Iran tana musanta abin da Trump ya fada game da bukatar Iran na gudanar da tattaunawa, kuma ba ta gabatar da wata bukata ta ganawa da Amurkawa ba.
Yayin ganawarsa da Fira ministan gwamnatin Isra’ila Benjamin Netanyahu da yammacin ranar Litinin, Trump ya yi ikirarin cewa an sanya ranar tattaunawa da Iran, yana mai cewa: Iraniyawa suna son tattaunawa da Amurka.
A wani bangare na jawabin nasa, Trump ya sake nanata ikirarinsa game da shirin makamashin nukiliyar Iran, yana mai cewa: Ya yi imani cewa Iraniyawa suna son ganawa da Amurka ne domin samun zaman lafiya, ya kara da cewa; An lalata shirin makamashin nukiliyar Iran gaba daya, kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta tabbatar da cewa an lalata wurin da Amurka ta kai hari a Iran.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike
Kotun Babban Majistare da ke Yaba ta bayar da umarnin a tono gawarwakin mutane 10 da gobara ta kashe a ginin Afriland Towers da ke Legas a ranar 16 ga Satumba, 2025, domin a gudanar da bincike a kansu.
Alkalin kotun, Mai shari’a Atinuke Adetunji ce ta bayar da umarnin a ranar Talata bayan ta samu labarin cewa an riga da binne wasu daga cikin waɗanda gobarar ta ritsa da su.
“Mai ƙorafi ya rubuta wa Gwamnatin Jihar Legas don neman izinin tono gawarwakin waɗanda suka mutu, sannan a gudanar da bincike a kansu,” in ji Mai Shari’a Adetunji.
Wannan umarni ya biyo bayan wata wasiƙa daga ofishin babban lauya Femi Falana da aka aike wa Babban Mai Kula da Gawarwaki na Jihar Legas, Mai Shari’a Mojisola Dada, a ranar 29 ga watan Satumba, 2025.
Femi Falana (SAN), ta hannun ofishinsa, ya shigar da ƙorafi ga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Legas, yana neman a gudanar da binciken gawarwaki don gano musabbabin mutuwar da kuma tabbatar da adalci.
A zaman farko na shari’ar, Mai Shari’a Adetunji ta umurci dukkan ɓangarorin da suka halarta da su gabatar da takardun da suka dace kafin zaman kotun na gaba.
Kotun ta kuma gayyaci hukumomi da kamfanoni da suka haɗa da bankin UBA da Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS), Ma’aikatar Kashe Gobara, Afriland Towers, United Capital, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), Hukumar Tsaro ta Jihar Legas, da sauran masu ruwa da tsaki.
Adetunji ta ƙara da umartar mai ƙorafi da ya tuntubi iyalan waɗanda suka mutu don gano waɗanda ke da niyyar a tono gawar ’yan uwansu domin a gudanar da binciken gawarwaki.
Ta kuma nemi shaidun gani da ido da su bayyana don bayar da bayani kan abin da ya faru.
Lauya Yahaya Atata daga ofishin Falana ya shaida wa kotu cewa zaman na ranar an shirya shi ne don haɗa dukkan masu ruwa da tsaki da kuma fayyace yadda za a gudanar da binciken gawarwaki.
Sai dai alkalin ta lura cewa lauyoyin ba su shirya sosai ba, kuma ta jaddada cewa binciken ba zai ci gaba ba sai an gabatar da dukkan takardun da ake bukata.
Wani lauya mai wakiltar ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu, A. O. Mema, ya shaida wa kotu cewa abokinsa, Peter Ifaranmaye, wanda shi ne manaja a Hukumar Tara Haraji ta Tarayya, an riga da binne shi.
Bayan wannan bayani, alkali Adetunji ta jaddada cewa yin binciken gawarwaki yana da matuƙar muhimmanci.
“Binciken gawarwaki muhimmin abu ne. Ba za mu iya gudanar da bincike ba sai an yi bincike don a gano hakikanin abin da ya faru,” in ji ta.
Kotun ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Nuwamba, 2025.
Gobarar ta tashi ne a ginin Afriland Towers, wani katafaren ginin kasuwanci da ke titin Broad a unguwar Legas Island, a ranar 16 ga watan Satumba, inda ta kashe akalla mutane 10 tare da jikkata wasu da dama.
Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da sassafe, kuma ta bazu cikin ginin da sauri kafin hukumomin kasha gobara su samu damar shawo kanta.