Wannan ya janyo tambayoyi kan ko za ta iya komawa nan take.

A lokacin da aka tambaye ta me take yi a lokacin da aka dakatar da ita, Sanata Natasha ta ce ba ta tsaya ba, har yanzu tana gudanar da ayyuka tare da wakiltar mutanenta.

“Na kasance ina aiki a duk lokacin. Na ci gaba da aiki kuma ina shirin gabatar da wasu dokoki a kan ma’adanai.

Ba zan iya miƙa su ga wani ba,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa duk da cewa ba ta halartar zaman majalisa, ta ci gaba da yin ayyukan ci gaba ga mutanenta.

“Fitar da ni daga majalisa ba kawai ni aka daƙile ba, an hana muryar Kogi ta Tsakiya fitowa fili,” in ji ta.

“Majalisar Dattawa ta hana mata da yara ‘yan Nijeriya samjn wakilci. Yanzu muna da Sanata mata guda uku kacal, alhali a baya muna da takwas.”

LEADERSHIP ta ruwaito cewa sanarwar dawowarta da aka shirya yi a ranar Talata ta tayar da hankula a majalisar, inda aka tsaurara tsaro kuma aka kawo motocin jami’an tsaro da dama.

Shige da fice daga harabar majalisar ya kasance a ƙarƙashin kulawar jami’an tsaro, inda ake bincikar motoci kafin ba su iznin shiga.

Ko da yake ba ta koma majalisar ba tukuna, Sanata Natasha ta jaddada cewa za ta ci gaba da yin aikinta.

“Ina da niyyar ci gaba da wakiltar Kogi ta Tsakiya da Nijeriya gaba ɗaya,” in ji ta.

“Ko na je majalisa ko ban je ba, zan ci gaba da sauke nauyin da ke kaina.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kogi ta Tsakiya Majalisar Dattawa

এছাড়াও পড়ুন:

Malaman Firamare Sun Janye Yajin Aiki A Abuja, An Umarci Su Koma Bakin Aiki

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za A Horas Da Jami’an Tsaron Sakkwato, Kaduna Da Benue Sabbin Dabarun Aiki
  • Malaman Firamare Sun Janye Yajin Aiki A Abuja, An Umarci Su Koma Bakin Aiki
  • ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Halaka Sojojin Mamaya Biyar Tare Da Jikkata Wasu Goma Na Daban
  • Dalilin da matan karkara a Kano suka fi son haihuwa a gida
  • Lauyoyin Majalisar Dattawan Nijeriya Sun Ƙaryata Natasha Kan Cewa Kotu Ta Ce Ta Koma Bakin Aiki
  • Sojoji Da Masu Gadin Gandun Daji Zasu Murkushe Masu Aikata Laifuka A Kwara
  • Yankin Kudu-Maso-Kudu Zai Cimma Matsaya Ɗaya Kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki – Sanata Dickson
  • Ranar Talata Mai Zuwa Zan Koma Zauren Majalisar Dattawa – Sanata Natasha
  • Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha