Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina
Published: 10th, July 2025 GMT
Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 30 a ƙauyukan Kadisau, Raudama, da Sabon Layi da ke Ƙaramar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.
Jami’an tsaron sun haɗa da ’yan sanda, sojoji, da rundunar sojin sama ta Najeriya.
HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya An gabatar da Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAANJami’an sun kai ɗauki ne bayan samun rahoton ’yan bindigar sun kai farmaki a lokaci guda a wurare daban-daban.
Amma, ’yan sanda uku da sojoji biyu sun rasa rayukansu a yayin artabu da ’yan bindigar.
Wani jami’in tsaro mai suna Ya’u Aliyu ya samu rauni.
Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasir Mu’azu, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba.
Ya ce gwamnatin jihar tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalan jami’an da suka rasu da kuma ragowar da abin ya shafa.
Ya ƙara da cewa iyalan waɗanda suka rasu za su samu tallafin gwamnati, kuma ba za a taɓa mantawa da sadaukarwarsu ba.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin kawo ƙarshen hare-haren ’yan bindiga da wanzar da zaman lafiya a jihar.
Ya roƙi al’umma da su kasance cikin shiri a koda yaushe kuma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.
Ya kuma ce bincike na ci gaba, kuma za a riƙa bayar da sabbin bayani a kai a kai.
“Ba za mu huta ba sai mun kawar da duk wani mai aikata laifi daga Jihar Katsina.
“Harkokin tsaro na ƙara inganta, kuma muna aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaron Tarayya domin tabbatar da tsaron kowa,” in ji Mu’azu.
“Da haɗin kanmu, za mu shawo kan wannan matsala kuma mu gina Katsina mai cike da zaman lafiya ga kowa da kowa.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Yan Sanda hari Jami an Tsaro Jami an tsaro jami an tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
AI Zai Maye Gurbin Ayyuka Miliyan 92 A Duniya – Farfesa Pate
A ƙarshe, Farfesa Pate ya yabawa gwamnatin tarayya bisa gina sabbin gine-gine a jami’ar kamar ginin Majalisar Jami’a, katangar jami’a, da ɗakunan kwana. Ya bayyana cewa dalibai 6,870 ne suka kammala karatu, ciki har da 91 da suka samu First Class da kuma 16 da suka kammala karatun digiri na PhD. Haka kuma, jami’ar ta karrama mutane biyar da digirin girmamawa saboda gudummawarsu ga ci gaban kasa da ilimi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp