Aminiya:
2025-07-09@17:26:54 GMT

Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista

Published: 9th, July 2025 GMT

Ministan Lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce Gwamnatin Tarayya na shirye-shiryen sake kara kudin wutar lantarki domin rage yawan bashin da bangaren lantarkin ke bi.

Bayanai dai sun nuna yanzu haka, bashin lantarkin da ake bi a Najeriya ya haura Naira tiriliyan hudu.

Amma a cewar ministan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki 300 a Abuja, yunkurin wani bangare ne na tabbatar da cewa bangaren lantarki ya tsaya da kafarsa.

Matar tsohon Gwamnan Adamawa ta sauya sheka daga PDP zuwa ADC Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda

Idan dai za a iya tunawa, duk da Karin kudin wutar da aka yi wa kwastomomin da ke tsarin Band A, mutane na ci gaba da korafin cewa ba sa samun isasshiyar wutar da ta kai ta kimar abin da suke biya.

Sai dai ministan ya ce yin karin na da muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya da kuma ci gaban kasa.

A cewarsa, “A yanzu haka, akwai tarin bashin da lamfanonin da ke samar da wutar ke bin bashi sakamakon cire tallafin lantarkin da gwamnatin ta yi, wanda yah aura Naira tiriliyan hudu a karshen watan Disambar bara.

“Tuni gwamnatin ta fara tsare-tsaren ganin cewa wannan bashin bai ci gaba da taruwa ba, shi ya sa ma take kokarin kara farashin wutar, sannan ta kirkiro da sabon tallafi ga masu karamin karfi a cikin masu amfani da wutar.

“Abin da hakan ke nufi shi ne gwamnati za ta kawo karshen tallafin da take biya, wanda hakan ke nufin za a sami karuwar farashin a dukkan matakai,” in ji Ministan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Karin kudin wuta Lantarki

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Sarkakiyar Dake Gaban Hadakar ADC — Atiku Ko Peter Obi

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

‘Yan Najeriya suna ci gaba da tafka muhawara a kan  wanda jamiyyar hadaka ta ADC zata tsayar takarar Shugaban Kasa a zaben 2027.

 

Yayin da wasu suke ganin Atiku Abubakar yana da dimbin magoya baya, wasu kuwa gani suke yi shi ma Peter Obi ba kanwar lasa bane.

Ko me zai faru idan daya daga cikin su ya samu tikitin tsayawa takara a 2027?

NAJERIYA A YAU: Mene ne tasirin naɗin Mataimaka na Musamman a rayuwar jama’a? DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan wannan lamari.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NAJERIYA A YAU: Sarkakiyar Dake Gaban Hadakar ADC — Atiku Ko Peter Obi
  • Sin Za Ta Gina Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Ingantaccen Lantarki
  • Kenya: Zanga-zanga Ta Tsayar Da Kai Komo A Birnin Nairobi
  • An Kaddamar Da Shirin Samar Da Wutar Lantarki A Jami’ar Kashere Gombe.
  • Kano ta sami rahoton cin zarafin yara 351 – NHRC
  • Gwamna Yusuf Ya Kaddamar Rabon Na’urorin Rarraba Lantarki 500
  • Bincike ya nuna ’yan Najeriya ba su gamsu da gwamnatin Tinubu ba
  •  Togo: An Yi Kiran Sake Yin Wata Sabuwar Zanga-zanagr Kin Jinin Gwamnati
  • Sheikh Kassim: Mayakan Hizbullah Mazajen Fagen Daga Ne