Aminiya:
2025-07-10@04:38:11 GMT

Ana zargin takalar faɗa tsakanin fadar Aminu Ado da Sanusi II

Published: 10th, July 2025 GMT

Tashin hankali ya sake kunno kai a Masarautar Kano, inda aka zargi wasu magoya bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da kutsawa cikin fadar Sarki Muhammadu Sanusi II ta Gidan Rumfa da ke Kofar Kudu.

Shaidu sun bayyana wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne lokacin da tawagar Sarki Aminu ke dawowa daga gaisuwar rasuwar attajirin ɗan kasuwa, marigayi Alhaji Aminu Ɗantata.

Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya

A wata sanarwa da kakakin masarautar Kano, Sadam Yakasai, ya fitar ya bayyana cewa Sarki Sanusi ba ya cikin fadar lokacin da abin ya faru ba.

“Sun fasa kofar shiga fadar, sun kai wa masu gadi hari, har suka raunata wasu.

“Haka kuma sun lalata motocin ‘yan sanda da ke wajen fadar. Aminu ya yi amfani da titin gidan Sarki maimakon ya bi hanyar Koki zuwa Nasarawa, inda yake zaune. Wannan ya nuna cewa da gangan ya nufi Gidan Rumfa.”

Yakasai, ya ƙara da cewa wannan ba shi ne karon farko da Sarki Aminu ke fakewa da hanyar Gidan Rumfa ba, yana jefa fargaba a zukatan mazauna unguwar.

Wani makusancin Sarki Sanusi, da ya nemi a sakaya sunansa ya ce harin ya faru ne da gozon bayan wasu daga cikin majalisar Sarki Aminu.

Ya ce wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta kafin tashin hankalin ya tabbatar da hakan, inda aka jiyo wani daga cikin majalisar yana tabbatar da abin da za su yi.

Tawagar Sarki Bayero ta musanta

Sai dai wani daga cikin tawagar Sarki Aminu Ado Bayero, Mukhtar Dahiru, ya ƙaryata zargin.

Ya ce: “Ni kaina ina cikin tawagar Sarki Aminu a lokacin. Mun dawo daga Koki ne bayan gaisuwar rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata. Sai dai a kusa da fadar Ƙofar Kudu muka tarar da wasu ɓata-gari da suka rufe hanya ɗauke da muggan makamai.

“Masoya Sarki ne suka tunkare su domin su ba mu hanya mu wuce.”

Ya ƙara da cewa babu wani hari da suka kai wa jami’an tsaro a fadar Sarki Sanusi, sai dai ‘yan sanda ne suka yi amfani da barkonon tsohuwa domin shawo kan lamarin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Aminu Ado Bayero Kofar Kudu Magoya Baya Masarautar Kano Sarkin Kano Sarki Aminu

এছাড়াও পড়ুন:

An Yi Hasashen Karuwar Tattalin Arzikin Kasar Sin Za Ta Zarce Yuan Tiriliyan 35 Tsakanin 2021 Zuwa 2025

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yi Hasashen Karuwar Tattalin Arzikin Kasar Sin Za Ta Zarce Yuan Tiriliyan 35 Tsakanin 2021 Zuwa 2025
  • Peter Obi Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Aminu Dantata
  • An kama ɓarayin babura a Gombe
  • ‘ADC za ta mayar da APC jam’iyyar adawa a 2027’
  • ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Halaka Sojojin Mamaya Biyar Tare Da Jikkata Wasu Goma Na Daban
  • Kakakin Rundunar Izzuddeen Qassam ya Bayyana Yadda Suka Yi Kofar Rago Ga Sojojin Mamayar Isra’ila
  • Falasdinawa 13 Ne Suka Yi Shahada Wasu Da Dama Suka Jikkata A Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza
  • Sojoji Sun Fatattaki Ƴan Bindigar Da Suka Zo Sace Wani Ɗan China
  • Miliyoyin Yan Najeriya Ne Suka Gudanar da Tattakin Ashoora Wasu Kuma A Makarantunsu…