Aminiya:
2025-07-09@19:07:43 GMT

An gabatar da Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAAN

Published: 9th, July 2025 GMT

An gabatar da Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, a matsayin Shugaban Kwamitin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN).

Wannan naɗin ya biyo bayan murabus ɗin da Ganduje ya yi daga shugabancin APC kwanan nan, inda ya bayyana cewa ya yi hakan saboda wasu muhimman dalilai na ƙashin kansa.

2027: Idan ADC na son lashe zaɓe dole ta bai wa ɗan Arewa takara — Okonkwo Biza: UAE ta ƙaƙaba wa ’yan Najeriya sabbin takunkumai

Jam’iyyar ta maye gurbinsa da Ali Bukar Dalori a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.

Gbenga Saka, mai bai wa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, shawara kan harkokin dijital, ya wallafa bidiyon bikin rantsar da Ganduje a shafin X.

Ganduje, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya kasance cikin kwamitin hukumar tare da wasu kamar su: Ms Olubunmi Kuku, Babbar Daraktar FAAN, Ms Dorothy Duruaka, Ahmed Ibrahim Suleiman.

Sauran sun haɗa da Nasiru Muazu, Omozojie Okoboh, TP Vembe da kuma Bridget Gold a matsayin sakatariyar kwamitin.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne, ya naɗa Ganduje shugaban wannan kwamitin tun a watan Janairun 2025.

A wajen bikin, Minista Festus Keyamo ya ce: “Muna sa ran wannan kwamitin zai taimaka wajen bunƙasa harkokin sufurin jiragen sama a ƙasar nan, haɗa yankuna daban-daban, da kuma kawo ci gaban tattalin arziƙi.

“Duk da ƙalubale kamar matsalar gine-gine da sauye-sauyen da ke faruwa a harkar jiragen sama a duniya.

“Ina da tabbacin ƙwarewarku za ta taimaka wajen cimma burin FAAN.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Filayen Jiragen Sama gabatarwa

এছাড়াও পড়ুন:

‘Abin da zai sa APC ba za ta taɓa mantawa da Ganduje ba’

Aminu Dahiru Ahmad, hadimin tsohon shugaban jam’iyar APC na kasa, Abudllahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar za ta gane ta yi kuskure kan saukarsa daga shugabancin.

A wata doguwar wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana takaicinsa kan rashin nuna wa Ganduje halasci, duk da irin ci gaban da ya kawo jam’iyar wanda ya ce ba a taba samun makamancinsa ba.

“Tarihin APC ba zai manta da Ganduje ba — Shi ya kai ta matsayin da take kai yanzu,” inji shi.

Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC An ƙayyade maki da shekarun shiga jami’a a Nijeriya

Aminu ya ba da misali da yadda aka dinga tururuwar shiga APC a lokacin mulkin Ganduje da kuma yadda Gwamnoni suka dinga sauya sheka, wanda ya ce ko hakan ya isa ya nuna kwarewarsa a fagen siyasa.

“A lokacinsa ne karon farko da wata jam’iyyar siyasa a Najeriya ta ga cancantar samar da wata dama da nufin magance matsalar shigar matasa a harkokin siyasa.”

A wani sakon da ya wallafa kafin wasikar, ya ce za su rama biki idan lokaci ya yi, kuma a nan ne za a gane Ganduje shi ne rufin asirin APC.

“Tinubu ya mana rauni sau daya, sau biyu, har sau uku. Allah Ya kai mu ranar ramuwa, ranar da za su gane cewa shi ne rufin asirinsu,” in ji shi.

A bayan nan ne dai tsohon gwamnan na Kano, Ganduje ya ajiye muƙaminsa na shugabancin jam’iyyar APC.

Duk da yake Ganduje ya ce rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus, wasu majiyoyi sun bayyana cewa rikicin siyasa a cikin jam’iyyar ne suka tilasta masa ajiye muƙamisa.

Ganduje ya zama Shugaban APC a watan Agustan 2023, a lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rawar Ganin Da BRICS Ke Takawa Wajen Samar Wa Kasashe Masu Tasowa ‘Yanci A Tsarin Gudanar Da Harkokin Kasa Da Kasa
  • ‘Abin da zai sa APC ba za ta taɓa mantawa da Ganduje ba’
  • Hukumar Abinci Ta Duniya ( WFP) Ta Jefa Wa Mutanane Kudancin Sudan Abinci Ta Sama
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce; An Rusa Hanyar Tattaunawa da Iran Kan Shirin Na Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • ADC: Tinubu Na Yunƙurin Raba Kawunan Masu Haɗaka Kafin Zaɓen 2027
  • Xi Ya Ajiye Furanni Ga Wadanda Suka Mutu Yayin Yakin Bijirewa Harin Japan
  • Gwamna Peter Mbah Ya Ƙaddamar Da Jiragen Kasuwanci 3 Na ‘Enugu Air’ Mallakin Jihar
  • Kasar Rasha Tana Ci Gaba Da Karya Kadarin Kasashen Turai A Yakin Da Suke Yi A Ukraine  
  • Ƴan Arewa Za Su Yi Murna Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Peter Obi