A Jiya Laraba Ce Iran Take Bukukuwan Cika Shekaru 78 Da Kwatar Kamfanin Man Fetur Na Kasar Daga Hannun Turawan Burtaniya
Published: 20th, March 2025 GMT
A ranar 19 ga watan Maris na ko wace shekara ne mutanen Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da mutanen kasar tare da taimakon gwamnatin lokacin suka sami nasarar kwace kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar, daga hannun wani kamfanin mai na kasar Burtaniya suka maida shin a kasa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce , wannan rana abin alfakhari ne ga mutanen kasar, don bayan haka ne kasar ta sami ikon kawo ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma shimfida harsashen samun yencin kasar daga hannun kasashen yamma wadanda suka mamaye bangarori da dama a cikin al-amuran kasar.
A ranar 19 ga watan Maris na shekara ta 1951 ne, wato shekaru 78 da suka gabata, firai ministan kasar Iran na lokacin Dr Muhammad Musaddiq tare da taimakon malaman addini ya sami nasarar kwace kamfanin man fetur na kasar daga hannun turawan ingila ya maida shi na kasa.
Majalisar dokokin kasar Iran ta amince da dokar maida kamfanin ya zama ta kasa a ranar 17 ga watan Maris na shekara ta 1951, sannan majalisar dattawan kasar ta amince da Ita a ranar 19 ga watan Maris na shekarar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ga watan Maris na
এছাড়াও পড়ুন:
An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja
An gano gawar wani malamin makarantar Islamiyya kuma mahaifin ’ya’ya bakwai, Malam Awwal Yakubu, a cikin wani kango da ke rukunin gidaje na Talba a birnin Minna, na Jihar Neja.
Malam Awwal, yana da makarantar Islamiyya a unguwar Barikin-Saleh, an neme shi sama ko ƙasa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata.
’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar BeninAn gano gawarsa ne da safiyar ranar Lahadi.
Rahotanni sun nuna cewa an ƙone al’aurarsa, sannan an samu kwalin ashana a gefen gawarsa.
Shugaban al’ummar yankin, Malam Mahmud Dalhatu Iya, ya shaida wa Aminiya cewa iyalan mamacin sun riga sun gano gawar kuma an riga an binne shi.
Ya ce, “An sanar da ni cewa an ga wata gawa ta lalace a wani gini da ba a kammala ba a cikin rukunin gidajenmu.
“Mun kai wa ’yan sanda rahoto. Muna nan lokacin da wani ya zo ya ce shi abokin mamacin ne, ya kuma ya ɓace tun ranar Alhamis. An yi wa gawar sutura don yi mata jana’iza a lokacin da nake magana da ku.”
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, “A yau, 7 ga watan Disamba 2025, da misalin ƙarfe 10 na safe, an samu rahoto cewa an ga gawa a bayan rukunin gidaje na Talba da ke kan titin Kpakungu.
“Jami’an ’yan sandan Kpakungu sun je wajen kuma sun gano gawar ta lalace cikin wani gini da ba a kammala ba.
“Daga bisani iyalansa suka tabbatar da cewa Auwal Yakubu ne, mai shekaru 45, mazaunin wannan yanki.”
Ya ƙara da cewa, “Ana zargin cewa an jefar gawar ne a wajen, domin an ruwaito ya ɓace tun a ranar 4 ga watan Disamba kafin a gano shi da safiyar yau.
“An kai gawar asibiti, kuma an fara bincike don gano musabbabin rasuwarsa.”