Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu
Published: 4th, April 2025 GMT
Fitaccen malamin addinin Islama da ke Jihar Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya riga mu gidan gaskiya.
Almajiransa sun tabbatar wa Aminiya cewa ya rasu ne a gidansa da ke Bauchi inda za a yi jana’izarsa a safiyar wannan Juma’ar.
Malamin ya yi fama da rashin lafiya inda gabanin watan Ramadana ya fita neman magani a ƙasashen Masar da Saudiyya.
Fitowarsa ta ƙarshe ita ce ranar Idin ƙaramar Sallah da ta gabata, inda ya yi huɗuba kan muhimmanci haɗin kai a tsakanin musulmi.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya
Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya ta naɗa Sheikh Bashir Aliyu Umar a matsayin shugabanta bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah.
Wata sanarwa da majalisar ta fitar a yau Laraba ta ce an amince da shuagabancin Dokta Bashir ne kai-tsaye saboda kasancewarsa mataimakin shugaba.
A ranar Litinin ne Sheikh Hadiyyatullah ya rasu yana da shekara 81 a Jihar Osun.
“Nan gaba za a sanar da mataimakin shugaban,” in ji sanarwar da Nafiu Baba Ahmed ya sanya wa hannu a matsayin sakataren majalisar.
Sheikh Bashir sanannen malami ne kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke Alu Avenue a Unguwar Nasarawa ta Jihar Kano.