Aminiya:
2025-07-09@07:19:36 GMT

Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja

Published: 18th, March 2025 GMT

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙwace wani fili mallakar sakatariyar Jam’iyyar PDP da ke Abuja.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun shugaban sashen kula da filaye na Abuja, Chijioke Nwankwoeze.

Nwankwoeze ya ce an yanke hukuncin ƙwace filin ne sakamakon gazawar babbar jam’iyyar adawar na biyan kudin gini na shekara shekara.

Wasiƙar ta ce PDP ta gaza biyan kuɗin tun daga ranar 1 ga watan Janairun 2006 zuwa 1 ga watan Janairun 2025, duk da sanarwar da hukumar gudanarwar babban birni (FCTA) ta wallafa a jaridu da dama tun daga shekarar 2023 kan buƙatar biyan kuɗaɗen.

Aminiya ta ruwaito cewa filin na Jamiyyar PDP na daga cikin filaye 4,700 da Ministan ya ƙwace a Abuja.

 

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Kano ta sami rahoton cin zarafin yara 351 – NHRC

Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC) a jihar Kano ta ce ta samu rahoton laifuka 351 na take hakkin yara daga cikin jimillar kararraki 446 da ta samu daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025.

 

Kodinetan NHRC na jihar Kano Alhaji Shehu Abdullahi ne ya bayyana haka a Kano.

 

Ya bayyana cewa daga cikin jimillar korafe-korafe 446 da aka samu a cikin watanni uku 351 na da alaka da take hakkin yara.

 

Ko’odinetan jihar ya yi nuni da cewa, sauran shari’o’in sun hada da tashin hankalin gida 19, 18 da suka shafi ‘yancin tattalin arziki da zamantakewa, da kuma biyar da suka shafi ‘yancin rayuwa.

 

 

“cikin zarge zargen har na Maita da sauran shari’o’in da suka shafi take hakkin dan adam”

 

 

A cewar Alhaji Shehu, yanayin zamantakewar al’umma a halin yanzu yana nuni da yadda ake tauye hakkin yara, wanda hakan ya nuna yadda ake kara yawaitar yaran da ke yin bara a tituna da kuma rayuwa cikin mawuyacin hali.

 

“Sakaci na iyali da al’umma shi ne babban abin da ke haifar da cin zarafin yara da kuma karuwar ayyukan aikata laifuka a tsakanin matasa.”

 

Ko’odinetan hukumar ta NHRC ya jaddada cewa, yayin da bakwai kawai daga cikin wadanda aka bayar da rahoton an aikata su ne ta hannun masu  fada aji kuma yana farywa a cikin gidajen aure.

 

“Iyali su ne tushen al’umma, al’umma kuma ita ce al’umma, saboda haka, duk wani cin zarafi a cikin iyali zai yi naso a kan al’umma baki daya.”

 

Ya kara da cewa “Lokacin da aka samu babban cin zarafi a cikin iyali, ba za a iya samun ci gaba mai ma’ana a cikin al’umma mafi girma ba.”

 

Alhaji Shehu ya ci gaba da cewa, daga cikin korafe-korafen da aka samu, an gudanar da cikakken bincike da kuma kammala shari’o’i 341, yayin da 105 ke ci gaba da sauraron karar.

 

Ya yi kira ga jama’a da su samar da zaman lafiya da juna tare da kai rahoton duk wani da ake zargi da take hakkin dan Adam ga hukumomin da abin ya shafa.

 

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, NHRC tana aiki ne a matsayin wata hanya mai zaman kanta don tabbatar da mutuntawa, kariya, da kuma inganta hakin bil’adama a Najeriya.

 

Khadija Aliyu

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Malaman Firamare Sun Janye Yajin Aiki A Abuja, An Umarci Su Koma Bakin Aiki
  • Tinubu Ba Zai Yarda Hayaniyar Siyasar 2027 Ta Ɗauke Masa Hankali Ba – Ministan Yaɗa Labarai
  • Malaman firamare sun janye yajin aiki a Abuja
  • ‘ADC za ta mayar da APC jam’iyyar adawa a 2027’
  • ASUU Ta Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Albashin Watan Yuni
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yace Mutanen Kasarsa Suna Cikin Shiri Don Kare Kansu Da Karfi
  • Kano ta sami rahoton cin zarafin yara 351 – NHRC
  • Elon Musk zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka
  • Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC
  • Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC