Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa
Published: 18th, March 2025 GMT
Bayan shafe kwanaki 40 har yanzu waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima ta Najeriy a(NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya ba su sako shi ba duk da cewa an biya kuɗin fansa.
Rahotanni sun nuna cewar an biya maƙudan kuɗaɗe don ganin an sako Janar Tsiga, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 5 ga watan Fabrairun da ya gabata a Ƙaramar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina.
Wata majiya ta kusa da iyalansa ta ce bayan kai kuɗin, sai da aka shafe mako guda kafin ’yan bindigar suka sake tuntuɓar iyalansa, inda suka haɗa su ta waya, sannan kuma suka sake neman ƙarin wasu kuɗaɗe.
“Saboda wasu dalilai gaskiya ba zan faɗi adadin kuɗin da aka biya ba amma kuɗaɗe ne masu yawan gaske,” a cewar majiyar.
Da farko dai waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Janar ɗin, sun buƙaci a ba su naira miliyan 250 a matsayin kuɗin fansa, sai dai an ci gaba ta tattaunawa da su.
Wasu bayanai na cewa akwai yiwuwar waɗanda suka yi garkuwa da shi sun sauya masa matsugunni.
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya ACF da kuma ta Dattijan Jihar Katsina KEF, sun buƙaci gwamnatin da kuma rundunar sojojin ƙasar, su matsa ƙaimi wajen ganin an kuɓutar da shi da sauran mutanen da aka yi garkuwa tare da su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: garkuwa da mutane Janar Tsiga yi garkuwa da
এছাড়াও পড়ুন:
Tehran ta yi kakkausar suka kan tsare Iraniyawa a Birtaniya
Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Birtaniya a birnin Tehran, biyo bayan tsare wasu ‘yan kasarta da dama ba bisa ka’ida ba a kasar.
Shugaban bangaren kula da sashen yammacin turai a ma’aikatar harkokin wajen kasar ya yi kakkausar suka da nuna adawa da matakin na gwamnatin Birtaniyya, da kuma zarge-zargen da ba su dace ba da ake yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Jami’in ya ce tsare ‘yan kasar Iran ya sabawa ka’idoji da dokokin kasa da kasa da kuma hakkokin bil’adama da aka amince da su, saboda an tuhume su ba tare da wata hujja ba.
Ya kara da cewa ‘yan kasar Iran da ake tsare da su, an kuma hana su harkokin ofishin jakadanci da kuma ba su kariya…
Jami’in na Iran ya jaddada cewa gwamnatin Birtaniyya ce ke da cikakken alhakin irin wadannan ayyuka, wadanda ake ganin suna da alaka da siyasa domin matsin lamba kan Iran.
A ranar Asabar an kama wasu mutane hudu ‘yan kasar Iran, kuma An tsare su ne a karkashin dokar ta’addanci, kamar yadda kafafen yada labaran Burtaniya suka ruwaito.