2025-11-10@02:56:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 413

«Buɗa baki»:

    Makarantar Kwalejin Kagara da ke Jihar Neja, wadda ta yi fice wajen yayi ɗalibai masu hazaƙa, yanzu ta zama kufai. A shekarar 2021, Boko Haram ta kai hari makarantar ta sace aƙalla dalibai da malamai 27. 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Jiya na...
    Ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, ya yi ƙoƙarin karya tarihin Kundin Tarihi na Duniya, na zane a fuska mafi yawa cikin mintuna uku. Ɗalibin ya samu tallafi daga kamfanin da ke yin taliyar yara Indomie, inda ya yi zane a fuskar mutum 17 cikin mintuna uku, wanda hakan ya ba shi...
    Fitaccen ɗan wasan gaban Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya kafa tarihin zama na farko a ƙungiyar da ya ci mata ƙwallaye 200. Griezmann ɗan asalin Faransa ya kafa wannan tarihin ne a ranar Talata yayin Gasar Zakarun Turai, inda Atletico ta lallasa Eintracht Frankfurt ta Jamus da ci 5-1. Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa...
    Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin soma karɓar haraji daga hannun mata masu zaman kansu waɗanda suka mayar da karuwanci sana’a. Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kuɗi da gyaran dokokin haraji, Taiwo Oyedele, ya ce kuɗaɗen da masu sana’ar karuwanci ke samu za a riƙe cire musu haraji a ƙarƙashin sabuwar dokar haraji ta...
    Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa FIFA ya sanar da matakin da ta ɗauka a kan tawagar ƙwallon Afirka ta Kudu, inda ta rage mata maki, sannan ta ci ta tarar kuɗi. Kwamitin ya bayyana cewa ƙasar ta karya doka ne ta hanyar amfani da ɗan wasa da bai cancanci buga wasan ba, a fafatawar...
    Gwamnatin Tarayya ta wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima NYSC. Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta...
    Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon tsari da ya danganci rajistar masu bautar ƙasa (NYSC) da manufofin hukumar da ke tattara bayanai kan ilimi wato NERD. A yanzu dai babu ɗalibin Nijeriya – daga jami’a ko kwalejin kimiyya da fasaha ko kwalejin ilimi, ko jami’o’in ƙasashen waje – wanda za a amince don samun...
    Wata ɗalibar aji biyu a sashen nazarin ƙwayoyin halittu da sunadarai na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja ta riga mu gidan gaskiya. Aminiya ta ruwaito cewa, Fatima Adamu Muhammad, ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani matsuguninta da ke wajen makarantar. ASUU ta bayar da wa’adin...
    Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi...
    Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi...
    Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki.   Yace An zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun...
    Jami’ar Bayero Kano (BUK) da ke Kano ta sanar da korar ɗalibai 57 saboda kama su da laifuka masu nasaba da maguɗin jarrabawa. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da darektan sashen kula da harkokin jarrabawa na jami’ar, Malam Aminu Wada Kurawa ya fitar. Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki...
    Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare a Nijeriya (NECO) ta jaddada cewa Jihar Kano ce ta fi kowace jiha samun nasara a sakamakon jarrabawar bana, tana mai ƙaryata rahoton da jaridar Premium Times ta fitar, wanda ya ce Jihar Abia ce ke kan gaba. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa rahoton...
    Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta yi zargin cewa tun daga shekarar 1899 Faransa take fafutikar tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel. Firimanistan Jamhuriyyar Nijar, Ali Lamine Zeine, ya yi wannan caccakar ce kan Faransa a ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a Babban Taron Majalisar Dinkin...
    Wani ɗalibi mai suna Ogbeche, ya kashe malaminsa Oshen, a makarantar sakandire da ke garin Ugboro, da ke Ƙaramar Hukumar Bekwarra a Jihar Kuros Riba. Rahotanni sun nuna cewa malamin ya yi ƙoƙarin raba faɗa tsakanin Ogbeche da wani ɗalibi. Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Matatar Ɗangote ta dakatar da sayar da...
    An gurfanar da wasu malamai biyu na wata makaranta ta Zariya Children School da ke yankin GRA Zariya, a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada bisa zargin lalata wata ɗalibar makarantar mai shekaru 11. Jami’in da ke gabatar da ƙara a gaban kotun, ASC Mustapha Abdulkadir, ya ce malamai biyu tare da wasu uku...
    A wajen ɗalibin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, zane ba kawai sha’awa ba ce kaɗai, face hanya ta shiga kundin tarihin duniya. A ranar 1 ga watan Oktoba, 2025, Collins zai shiga sahun tarihin duniya yayin da zai yi ƙoƙarin kafa tarihi har guda biyu na shiga kundin ‘Guinness World Record’ a fannin...
    Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta sanar da cafke wani mutum da ke yi mata sojan-gona yana yaudarar jama’a domin karɓar musu kuɗi. An cafke wanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 21 ga Satumbar 2025 a yankin Kofar Dawanau, sanye da kayan ’yan sanda, wanda bayanai suka ce ya daɗe yana aika-aikar. An yi...
    Wata Kotun Soji ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ka’ida ba a Maiduguri, Jihar Borno. Kotun sojin ƙarƙashin jagorancin Birgediya-Janar Mohammed Abdullahi, ta bayyana cewa an yanke wa mutum uku daga cikin sojojin huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai yayin da aka...
    An kashe wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani shingen bincike, inda suka ɗauke bindigarsa bayan sun halaka shi a Jihar Taraba. Wata majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Tella, cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, lokacin da ’yan...
    Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Mazaɓar Pankshin ta Kudu, Laven Denty Jacob. A yammacin ranar Litinin aka yi garkuwa da shia gidansa da ke Anguwan Kagji, a Unguwar Dong, a Ƙaramar hukumar Jos ta Arewa. Wani na kusa da shi ya tabbatar wa manema labarai cewa...
    Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar dawowarta daga hutu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2025. Karin bayani na tafe..
      Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan ɗalibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da ɗalibai.   Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Kaduna domin ƙara wa ma’aikata da abokan hulɗarsu...
    Tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a Litinin ɗin nan a birnin Landan kamar yadda kafar labarai ta DW ta ruwaito. Bikin ɗaga tutar na zuwa ne kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta. CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsa a shirye ta ke, ta haɗa kai da APC, idan an shirye karɓar sharuɗansu. Kwankwaso, ya faɗi haka ne a gidansa da ke Miller Road a Kano, lokacin da ya karɓi baƙuncin tsohon jigon APC a jihar, Buhari Bakwana,...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari a Jihar Kaduna bayan halartar ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari. Da zuwansa, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da ɗan marigayin, Yusuf Buhari, tare da wasu suka tarbe shi. Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da...
    Sai yace “A’a ba haram ba ne, kawai dai mutanena ba su san shi ba ne.” Annabi (SAW) ya taɓa cewa kar a ci tafarnuwa a shigo masallaci, aka tambaye shi: “Ya Rasulallah haram ne?” Sai ya ce “A’a ba na haramta abin da Allah bai haramta ba, kawai dai ni ne ba na son...
    Bayanai na cewa, wannan munduwa mai ɗimbin tarihi, mallakin Fir’auna Amenemope ne, yayin da ta yi ɓatan-dabo a gidan tarihin da ake adana da ita. An rarraba hoton munduwar zinarin ga jami’an da ke aiki a kan iyakokin ƙasar daban-daban da suka haɗa da filayen jiragen sama da tashohin jiragen ruwa da zummar daƙile fasaƙaurinta...
    Wani ɗan kasuwa a Jihar Katsina mai suna Anas Ahmadu da matarsa, Halimatu wadda ke ɗauke da juna biyu, da kuma ’yarsu mai shekaru biyu, sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga, bayan sun shafe kwanaki 21 a hannunsu. An sako su ne a daren ranar Laraba bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan 50, kamar yadda...
    Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025. Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci. Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati...
    A cewarsa, ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajistar jarrabawar; maza 685,514 da mata 681,696. Daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarrabawar, waɗanda suka haɗa da maza 680,292 da mata 678,047. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Rikicin kwamitin gudanarwa da malaman Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bida (Bida Poly), ya ƙara ƙamari bayan da makarantar ta dakatar da ayyukan Kungiyar Malamai (ASUP) sannan ta kawo sojoji domin kula da jarrabawa da dalibai ke gudanarwa. Ƙungiyar ASUP reshen kwalejin ta shiga yajin aiki mara wa’adi, domin neman a biya su alawus...
    Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani ɗan ƙasar Indiya tare da wasu mutane uku bisa zargin shigo da ƙwayoyin Tramadol da aka ƙiyasta darajarsu ta kai naira biliyan uku (N3bn) zuwa cikin ƙasar. A cewar NDLEA, wannan shi ne kamen ƙwayoyi mafi girma da hukumar ta yi a...
    Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO) ya ƙaryata zargin da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya yi masa, dangane da mutuwar wasu marasa lafiya sakamakon katse wutar lantarki da aka ce kamfanin ya yi. Asibitin na AKTH ya bayyana damuwarsa a ranar Lahadi kan abin da ya kira abin takaici yana mai...
    Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.   An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar...
    Liɓerpool ce mai riƙe da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi a tarihin gasar premier ta ƙasar Ingila. Ga jerin ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan  ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a cikin ƙungiyoyin da...
    Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fara samun wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 24 ba tare da ɗaukewa ba. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya ƙaddamar da sabbin ɗakunan horo da ɗakin kwana a Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Ƙasa (NAPTIN). Gwamna ya...
    Gwamnatin Belarus ƙarƙashin jagorancin Shugaba Alexander Lukashenko ta saki fursunoni siyasa 52 ciki har da fitaccen ɗan adawa, Mikola Statkevich da kuma ɗan jarida Ihar Losik, a wani yunƙuri da aka danganta da ruwa da tsakin Amurka. Shugaban Lithuania, Gitanas Nauseda, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X (Twitter), yana mai cewa: “Mutum 52...
    Wata babbar kotu a Abuja ta yanke wa Mahmud Muhammad Usman (Abu Bara’a), ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan kaso. Abu Bara’a wanda Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta gurfanar a ranar Alhamis, ya amsa laifin gudanar da harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya ba...
    Wata budurwa mai shekaru 24 mai suna Kelechi Ebubechukwu, ta rasu a cikin wani yanayi da mai daure kai a gidan saurayinta da ke Gwagwalada, Babban Birnin Tarayya Abuja. Wani ƙwararren masani kan tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba. A cewarsa,...
    Hukumar Hana da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta cafke buhuna uku da kuma sinki 150 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 112. Bayanai sun ce an kama kwayoyin ne bayan wani hatsarin mota da ya faru a Gadar Tamburawa da ke kan hanyar Zariya zuwa Kano. Wannan na...
    Wata kotu da ke ƙasar Ghana ta yanke wa ’yan Najeriya uku hukuncin ɗaurin shekaru 96, bayan samun su da laifin satar mota a birnin Kumasi na ƙasar. Kotun dai ta samu Francis Friday da Linus Agwazie da kuma Russell Ekenze ne da laifin a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke neman a kori ’yan...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta sanar da ceto wani ɗan ƙasar Masar da wasu da ba a san ko su wane ba suka yi garkuwa da shi. Kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Talatar nan a Ibadan, babban birnin jihar. DSS...
    Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya buƙaci jami’an tsaro da su riƙa ɗaukar duk wani infoma da ke bayar da bayani ga ’yan bindiga a matsayin abu ɗaya da babu wani bambanci a tsakaninsu. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ƙananan hukumomin Wurno da Rabah a ranar Litinin da ta...
    Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da ma’aikatan gwamnati, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya, ta sake duba mafi ƙarancin albashi, domin Naira Naira 70,000 da ake biya yanzu ba ta isa wajen tafiyar da al’amuran yau da kullum. A cewarsu tashin farashin kayan abinci, sufuri, haya, da wutar lantarki ya ƙara jefa su cikin wahalar da rayuwa....
    Tsagin Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya ƙi amincewa da korar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Oginni Sunday ya raba wa ’yan jarida ranar Asabar. Musulman Kudancin Kaduna sun zargi manyan yankin da juya...
    Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari yankin Okpella, da ke Ƙaramar Hukumar Etsako ta Gabas, a Jihar Edo, inda suka kashe wasu jami’an tsaro. Sun kashe jami’an Sibil Difens guda takwas sannan suka yi garkuwa da wani ma’aikacin ƙasar China. APC ta yi barazanar hukunta “Yaran Badaru” a Jigawa...
    Iyayen ɗalibai a sassan arewacin Najeriya sun bayyana damuwarsu kan yadda ake ta ƙara kuɗin makaranta da kuma tsadar littattafai a kowace shekara, da sauran hanyoyin da suka ce makarantu ke tatsar kuɗi a hannunsu. Wasu makarantu masu zaman kansu kan tilasta wa iyaye sayen littattafai daga wurinsu kawai, alhali a kasuwa ana samun su...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kogi ta kama wata budurwa mai suna Charity Williams ’yar shekaru 23, wadda aka same ta da kuɗi Naira miliyan 2,047.500 da miyagun ƙwayoyi da kuma bindigar fistol. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jami’anta da ke aiki da sashin Okene a Ƙaramar hukumar Okene a jihar,...
    Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, ta amince za ta biya dukkanin kuɗaɗen jinyar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Nata’ala, wanda ke fama da ciwon daji. Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana ne, ya bayyana haka lokacin da ya kai masa ziyara a gidansa da ke Potiskum. Gwamnatin Sakkwato ta ba...