Kwamitin Tsaron Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza
Published: 6th, November 2025 GMT
Kwamitin Tsaro Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka ta bukaci duba kudurin da aka gabatar na neman kafa rundunar kasa da kasa a Gaza
Rahotannin daga Amurka sun bayyana cewa: Gwamnatin Amurka ta Trump tana neman amfani da rikicin Gaza wajen kwace makaman kungiyar Hamas da take amfani da ramuka wajen yakar ‘yan sahayoniyya, don aiwatar da wani tsari na kwace makamai daga hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa.
A ƙarƙashin tutar tsaro da kwanciyar hankali, Amurka, da kuma Isra’ila, suna ƙoƙarin kafa sabon tsari a Gaza wadda ke neman murkushe ‘yan gwagwarmaya, tare da tabbatar da tsarin babakeren ‘yan mamaya karkashin wani tsari mai sauƙi, da zai buɗe sabon babi na iko a kan yankin.
A tsakiyar tambayoyi game da manufofin Amurka da Isra’ila game da makomar yankin Gaza, Amurka na gabatar da daftarin kuduri ga Kwamitin Tsaro don tallafawa shirin shugaban Amurka Donald Trump, wanda ake tallata shi a matsayin shirin zaman lafiya ga yankin Gaza.
An rarraba daftarin, wanda ke kira da a kafa rundunar ƙasa da ƙasa ta wucin gadi a yankin, ga membobin Kwamitin Tsaron, da kuma Saudiyya, Masar, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Turkiyya, a hukumance, domin samun goyon bayan yankin, a cewar tawagar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya. Amurka ta yi da’awar cewa; Manufar ita ce don kawo karshen yakin da kuma sake gina Gaza, amma daftarin kudurin ya ba ta cikakken iko ta gudanar da yankin ta hanyar rundunar zartarwa wadda ba ta da cikakken iko a karkashin ikon Majalisar Dinkin Duniya kuma tana aiki tare da Masar da Isra’ila. Haka kuma tana goyon bayan abin da ake kira Majalisar Zaman Lafiya, wacce Trump ke jagoranta, don gudanar da harkokin mulki na wucin gadi da sake gina Gaza har zuwa karshen shekara ta 2027.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku A Kudancin Lebanon November 6, 2025 Sayyid Muqtada al-Sadr Ya Fadakar Da Magoya Bayansa Kwanaki Kafin Zabe A Iraki November 6, 2025 Araghchi : Yakin kwanaki 12 ya bamu babban darasi November 6, 2025 Putin : zamu dauki mataki idan Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya November 6, 2025 Iran, China da Rasha sun tattauna gabanin taron Gwamnonin IAEA November 6, 2025 Shugabannin Iran Da Faransa Sun Yi Wata Tattaunawa Ta Wayar Tarho November 6, 2025 Najeriya Ta Sake Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar November 6, 2025 Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya November 6, 2025 Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa
Wata majiya ta hizbbulla ta fadawa gidan talabijin din al-hadatha cewa kungiyar tana nan kan bakanta na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka sanyawa hannu tsakaninta da isra’ila musamman a yankunan kudancin kasar da kuma tekun litani
Duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan decembar shekara ta 2024 amma akwai fargaba sosai a iyakokin labanon da Isra’ila , sai dai hizbullah ta fitar da sanarwa a baya bayan nan wanda ke nuna shirinta na mayar da martani mai tsanani idan israila ta tsokaneta, duk da kasashen yamma na kokarin ganin an kawar da makamai da kuma rage tasirinsu, adaidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yiyuwar sake barkewar wani rikici
Ministan harkokin wajen kasar faransa Jean-neol barrot ya bayyana cewa kasarsa na goyon bayan kwabe makaman hizbullah kuma yayi kira ga isra’ila da ta janye daga wurare biyar masu muhimmanci a kudancin labanon.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Ta yi Kan Shirin Nukuliyarta November 4, 2025 Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar November 4, 2025 Ribadu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya kan barazanar Trump November 4, 2025 Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon November 3, 2025 Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha November 3, 2025 An Sami Tsaikon Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Tanzania Saboda Rikicin Zabe November 3, 2025 Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Nablus Da Khalil November 3, 2025 Jagora: Sabanin Jamhuriyar Musulunci Da Amurka Daga Tushen Manufa Ne Ba Sama-sama Ba November 3, 2025 Turkiyye na karbar taron Kasashen Musulmi Kan Halin Da Ake Ciki A Gaza November 3, 2025 Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci