Mahara sun kashe ɗan sanda, sun ɗauke bindigarsa a Taraba
Published: 23rd, September 2025 GMT
An kashe wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani shingen bincike, inda suka ɗauke bindigarsa bayan sun halaka shi a Jihar Taraba.
Wata majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Tella, cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, lokacin da ’yan bindigar suka yi wa shingen binciken ƙwanton ɓauna.
An ce maharan sun harbi ɗan sandan ne a kansa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take, lamarin da ya sa sauran abokan aikinsa da ke wurin suka tsere.
Bayan sun yi kisan, ’yan bindigar sun ɗauke bindigar marigayin sannan suka tsere daga wurin.
Kakakin rundunar ’yan sandan Taraba, ASP Leshen James, bai ɗaga wayar kiran da aka yi masa ba kuma bai amsa saƙon da aka tura masa dangane da lamarin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Ɗan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa
Wata kotu a Ƙasar Jamus ta yanke wa wani ma’aikacin jinya hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same shi da laifin kashe marasa lafiya 10 da kuma yunƙurin kashe ƙarin wasu 27 ta hanyar yi musu allurar guba.
Kotun da ke birnin Aachen a yammacin Jamus, ta tabbatar da cewa mutumin mai shekaru 44 ya aikata laifukan ne tsakanin watan Disamban 2023 zuwa Mayun 2024 a asibitin Wuerselen.
Sama da gidaje 8,000 za su samu wutar lantarki daga hasken rana a Gombe Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a IndonesiaKotun ta bayyana cewa laifin da ya aikata babban laifi ne, wanda zai hana shi samun ’yanci bayan shekaru 15 kamar yadda ake yadda a irin waɗannan shari’o’in.
Ba a bayyana sunan mutumin ba, amma masu gabatar da ƙara sun ce yana “wasa da rayuwar marasa lafiyar” da yake kula da su.
Lauyansa ya roƙi kotu ta wanke shi lokacin da aka fara shari’ar a watan Maris.
Masu gabatar da ƙara sun ce mutumin yana yi wa marasa lafiya, waɗanda mafi yawansu tsofaffi ne, allurar magunguna masu sa barci da rage zafi don rage wahalar aikinsa a lokacin dare.
Sun kuma bayyana cewa mutumin yana da matsalar halayya, ba ya nuna tausayawa ga marasa lafiya, kuma bai nuna nadama ba a lokacin shari’ar.
Haka kuma, sun ce yana amfani da morphine da midazolam, wani magani da ake amfani da shi a wasu lokuta wajen aiwatar da hukuncin kisa a Amurka.
An kuma sake zarginsa da yin aiki ba tare da bin ƙa’ida ba, da kuma rashin nuna ƙwazo a aikinsa.