Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau
Published: 5th, November 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce zai ci gaba da yin siyasa matuƙar yana numfashi a doron duniya.
Shekarau ya bayyana cewar siyasa wata babbar hanya ce ta hidima wa jama’a.
Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a KanoYayin da yake hira da ’yan jarida a Kano a yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa na cika shekaru 70, Shekarau, inda ya ce gina siyasarsa ne bisa tafarkin addini da ɗabi’a.
“Siyasata addinina ce, addinina kuma siyasata ce. Shiga cikin tsarin samar da shugabanni na gari masu gaskiya hidima ce ga jama’a kuma wannan ibada ce a Musulunci,” in ji shi.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa, siyasarsa ba ta da nasaba da son kai, sai dai niyyar ganin an samar da shugabanni masu adalci da kishin al’umma.
“Matukar ina da ƙarfi, zan ci gaba da bayar da gudunmawa. A gare ni siyasa ba aiki ba ne da ake daina yi; nauyi ne na rayuwa gaba ɗaya,” in ji shi.
Shekarau, wanda ya mulki Jihar Kano daga 2003 zuwa 2011, ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su haɗa kai domin ƙarfafa dimokuraɗiyya.
Ya kuma yi kira ga shugabanni su mayar da hankali kan matsalolin rashin tsaro, talauci da yunwa.
Ya kuma yaba wa jam’iyyar PDP bisa juriyarta inda ya bayyana cewar har yanzu tana taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya.
Ya kuma yi wa makomar siyasar Najeriya fatan alheri, tare da jadadda cewa zai ci gaba da goyon bayan kowace gwamnati don samar da zaman lafiya da jin daɗin ’yan ƙasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ranar haihuwa Shekaru Siyasa tsohon gwamna
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Yaba Da Tasirin Shirin NG-CARES A Jihar Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na fadada ayyukan ci gaban karkara, tare da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma.
Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin jami’in kula da shirin rage radadin illar da annobar cutar Korona ta haifar, wato (NG-CARES), Dakta Abdulkareem Obaje, wanda ya kai masa ziyara ta ban girma a Dutse.
Dakta Obaje ya yaba wa gwamnan da gwamnatin jihar Jigawa bisa goyon bayan da suke bai wa shirin NG-CARES tun daga lokacin da aka ƙaddamar da shi a shekarar 2021.
Ya bayyana cewa an kirkiro shirin ne a shekarar 2020 sakamakon tasirin annobar COVID-19, domin taimaka wa jihohi su farfaɗo da tattalin arziƙin karkara da tallafa wa marasa ƙarfi.
“Shirin NG-CARES ya kai shekaru huɗu yana gudana, kuma mun biya jihohi kuɗaɗe har zuwa dala miliyan 696, inda aka taimaka wa mutane kusan miliyan 70 a fadin ƙasar nan.” In ji Dakta Obaje.
Ya ƙara da cewa shirin, wanda ya fara da jimillar dala miliyan 750, ya ba da dama ga jihohi irin su Jigawa su taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da ayyuka da suka taɓa rayuwar jama’a kai tsaye.
Dakta Obaje ya kuma bayyana cewa sabon zagaye na shirin, NG-CARES 2.0, zai fara aiki nan ba da jimawa ba.
A nasa jawabin, Gwamna Namadi ya gode wa tawagar NG-CARES bisa ziyarar da suka kai masa, tare da bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen da suka fi tasiri wajen kai tallafi kai tsaye ga al’umma mafi ƙaranci a Jihar Jigawa.
“NG-CARES shi ne shirin da ya fi taɓa rayuwar jama’armu kai tsaye.” In ji shi.
Ya tunatar da yadda ya yi ƙoƙari wajen ganin an ci gaba da aiwatar da shirin a matakin Majalisar Gwamnonin Najeriya (NGF) da kuma Babban Bankin Duniya (World Bank).
“Ina iya cewa ba tare da wata shakka ba, NG-CARES 2.0 ra’ayinmu ne, domin mu ne muka nemi a ci gaba da shirin.” In ji Gwamna Namadi.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa shirin domin ƙarfafa hanyoyin kyautata rayuwa da kuma inganta tsaron zamantakewa a tsakanin jama’a.
Ziyarar ta kasance wani ɓangare ne na zagayen da ofishin NG-CARES ke yi a fadin ƙasa domin tattara rahotanni, jin ra’ayoyin jama’a, da kuma nuna nasarorin da aka samu yayin da ake shirin kaddamar da NG-CARES 2.0.