Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa
Published: 6th, November 2025 GMT
Kwamishinan lafiya na Jihar Adamawa, Dokta Felix Tangwami ya bayyana cewa, cutar kwalara a Ƙaramar hukumar Mubi ta yi sanadin mutuwar mutane 10, inda ya buƙaci mazauna yankin da su kula da tsaftar jikinsu.
Da yake yi wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) bayani a Yola ranar Laraba, Tangwami ya ce marasa lafiyan sun mutu ne a gida maimakon a cibiyoyin lafiya.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ɗauki matakin gaggawa don daƙile ɓarkewar cutar.
“Tun daga farko, mun ɗauki matakin gaggawa a kan lamarin, kasancewar mu a can, kuma ba za a iya musanta hakan ba,” in ji shi.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, waɗanda suka ziyarci cibiyoyin kiwon lafiya sun samu kulawa, inda aka kwantar da majinyata 25 a ranar Talata 4 ga watan Nuwamba, yayin da wasu da dama kuma an sallame su tare da wayar da su kan harkokin tsafta.
Ya bayyana cewa, an tura jami’an kula da cututtuka na jihar, da Daraktan kula da cututtuka a Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko, da masu aikin sa-kai zuwa Mubi domin gudanar da ayyuka da kuma wayar da kan jama’a.
Sun kuma gano waɗanda abin ya shafa a cikin unguwanni don tabbatar da sun samu kulawar lafiya.
Tangwami ya kuma yi kira ga shugabannin gargajiya da su goyi bayan ƙoƙarin gwamnati ta hanyar ƙarfafa gwiwar mazauna yankin da su gaggauta neman magani a cibiyoyin lafiya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Kano Ya Yaba Da Matakin Da Sojoji Suka Dauka kan Matsalar Tsaron Tsanyawa
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa rundunar Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa gaggawar daukar mataki kan hare-haren ‘yan bindiga da suka faru a wasu sassan jihar.
Gwamnan ya yi wannan yabo ne a lokacin da Babban Hafsan Runduna ta 1, wato GOC 1 Division da ke Kaduna, Major Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, ya kai masa ziyara a Gidan Gwamnati Kano.
Gwamna Yusuf ya bayyana jin dadinsa da yadda sojoji ke gudanar da aikinsu cikin kwarewau, jajircewa da kishin kasa, tare da bayar da tabbacin ci gaba da hadin kai tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro. Ya kuma gode wa Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu, bisa nada manyan hafsoshi masu kwarewa da suka himmatu wajen yaki da rashin tsaro.
Da yake jawabi, Janar Wase ya ce ya zo Kano ne domin duba yanayin tsaro a Shanono da Tsanyawa, inda aka yi hare-hare a kwanakin baya.
A cikin matakan tallafi, Gwamna Yusuf ya bayyana ba da gudummawar motocin Hilux guda 10 da babura 60 ga Rundunar Hadin Gwiwa da ke aikin tsaro a yankunan da abin ya shafa.
Abdullahi Jalaluddeen/Kano