Aminiya:
2025-11-04@22:41:56 GMT

HOTUNA: Mun kori jami’ai fiye da 100 cikin shekara guda — DSS

Published: 5th, November 2025 GMT

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa ta sallami jami’anta fiye da 100 a tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025, a wani yunƙuri na aiwatar da gyare-gyare a cikin hukumar.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, DSS ta ce jimillar jami’ai 115 ta sallama daga aiki saboda dalilai daban-daban da suka shafi aiwatar da tsare-tsaren sabunta tsarin aiki.

Fitaccen ɗan wasan tseren motoci Jenson Button zai yi ritaya Barazanar Trump: Ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Nijeriya — Tuggar

Sanarwar wadda ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce an fitar da sunaye da hotunan jami’an da abin ya shafa domin ankarar da jama’a.

“A wani ɓangare na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a hukumar DSS, an sallami jami’ai 115. Don haka ana gargaɗin jama’a da su guji yin hulɗa da waɗannan mutanen da aka sallama daga aiki,” in ji sanarwar.

Hukumar ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na tsaftace hukumar da tabbatar da ingantaccen aiki da gaskiya a tsakanin jami’anta.

Fuskokin wasu daga cikin jami’an da DSS ta sallama daga aiki

 

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan

 

“Wannan yajin aikin yana nan yana gudana, har sai an biya duk buƙatunmu mafi ƙaranci,” in ji shi.

 

NARD ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a duk faɗin ƙasar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati na cika jerin “mafi ƙanƙancin buƙatunta.” Wannan matakin dai tuni ya riga ya kawo cikas ga ayyuka a asibitoci mallakar gwamnatin tarayya da na jiha a faɗin ƙasar.

 

A halin yanzu, Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, a cikin wata sanarwa da Shugaban Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Alaba Balogun ya fitar, ya nace cewa, gwamnati ta saki kuɗaɗe kuma tana ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙwadago don ganin an kawo ƙarshen yajin aikin ƙungiyar NARD.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi November 3, 2025 Manyan Labarai Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya November 2, 2025 Manyan Labarai Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba November 2, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma
  • An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa
  • Uba Sani Ya Kaddamar Da Gidaje 100 Ga Waɗanda Rikici Ya Shafa A Jihar
  • Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT
  • NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan
  • Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazanar Sa Ga Nijeriya
  • Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon