Kungiyoyin da suka yi hadin gwiwar shigar da karar sun hada da Interfaith Partners for Peace and Development, Fityanul Islam of Nigeria, Sairul Qalbi Foundation, Tijjaniyya Youth Enlightenment Initiative, Hablullahi Mateen Foundation, Dariqa Qadiriyya of Nigeria, Kadiriyya Youth Awareness, Kadiriyya Riyadul Janna Kofar Na’isa, Ashabul Kahfi Foundation, da Majmau Ashabul Yameen.

 

LEADERSHIP ta ruwaito cewa, takaddamar da ta shafi Malam Lawan Triumph ta fara ne a watan Satumba bayan da wasu ƙungiyoyin addini suka ɗauki wasu wa’azozinsa a matsayin ɓatanci ga Annabi SAW, wanda ya haifar da cece-kuce da muhawara a faɗin jihar. Wannan lamari ya sa gwamnatin jihar ta shiga tsakani ta hannun Majalisar Shura ta Jiha, wadda aka ba da umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen.

 

Bisa umarnin gwamnati, Majalisar Shura bayan ta tantance wa’azozin malamin, sannan daga baya ta gayyace shi don zaman tattaunawa.

 

Tun bayan zaman, har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati kan sakamakon zaman da kwamitin Shura ya yi akan Malam Triumph.

 

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, gwamnatin Jihar Kano ko rundunar ‘yansanda ba su bayar da wani martani a hukumance kan karar ba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai November 5, 2025 Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu  November 5, 2025 Labarai Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista November 5, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu

Majalisar Dattawa ta dakatar da aikin tantance Dokta Kingsley Tochukwu Udeh, SAN, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa domin zama minista, sakamakon rashin gabatar mata da rahoton jami’an tsaro a kansa.

Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya ce ba za su ci gaba da tantancewar ba sai an samu cikakken rahoto daga hukumomin tsaro.

Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano

A ranar Talata ce Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar sunan Mista Udeh, ɗan asalin Jihar Enugu cikin wata wasiƙar neman sahalewarta.

“Ina farin cikin miƙa sunan Dokta Kingsley Tochukwu Ude, SAN, domin tabbatar da shi a matsayin minista. Ina fatan majalisar za ta yi la’akari da wannan buƙata cikin gaggawa kamar yadda aka saba,” in ji wasiƙar shugaban ƙasan.

Tinubu ya naɗa Udeh ne bayan murabus ɗin da tsohon Ministan Kimiyya, Uche Nnaji ya yi, bayan zargin da aka yi masa na gabatar da takardar shaidar kammala karatu ta bogi, wanda kuma shi ne minista ɗaya kacal daga Jihar ta Enugu

Mista Udeh wanda yanzu haka shi ne Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Enugu, ya shahara da ƙwarewa a fannin doka da kare haƙƙin ɗan Adam.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu
  • Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 
  • Gwamnan Kano Ya Yaba Da Matakin Da Sojoji Suka Dauka kan Matsalar Tsaron Tsanyawa
  • Kwamishinan Kano Na Ziyarar Tabbatar Da Zaman Lafiya A Wannan Kaka
  • ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu
  • Kotu ta sahale wa PDP gudanar da babban taronta a Ibadan
  • Abba ya umarci a riƙa gudanar da taron tsaro a ƙananan hukumomin Kano
  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano
  • Yadda matata ta ɓace a Abuja aka tsince ta a Sakkwato