Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar
Published: 7th, November 2025 GMT
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Sudan sun yi watsi da bukatar da kasar Amurka ta gabatar mata na dakatar da bude wuta, ta sha alwashin murkushe dakarun RSF wato kungiyar sojin sa kai ta kasar dake iko da mafiyawancin yankunan yammacin kasar Sudan
Wannan matakin yazo ne bayan taron gaggawa Da majalisar tsaron kasar ta gudanar wanda shugaban majalisar sojojin kasar janar Abdel fatah Al-burhan ya jagoranta inda suka sha alwashin murkushe dakarun kungiyar ta RSF.
Alburhan yayi alkawarin samun nasara yace wadanda suke yaki don kare hakkin alummarsu ba zaa yi nasara akan su ba,
Wadannan bayanan sun zo ne kwanaki kadan bayan da kungiyar ta RSF ta kwace garin al-fasher dake yammacin Darfur inda rahotanni suka bayyana irin kisan kare dangi da tayi da ya tilastawa fararen hula yin gudun hijira zuwa arewaci da kudancin Darfur.
Daga lokacin da yaki ya barke a watan Aprilun shekara ta 2023 tsakanin dakkarun kasar da dakarun kungiyar RSF an kashe dubban mutane kuma akalla mutane miliyan 13 ne suka tarwaste inda kungiyar RSF ke iko da jihohi 5 dake yankin Dafur
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jin Isra’ila . November 7, 2025 Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne November 7, 2025 Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar November 7, 2025 Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani November 6, 2025 Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu November 6, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza November 6, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku A Kudancin Lebanon November 6, 2025 Sayyid Muqtada al-Sadr Ya Fadakar Da Magoya Bayansa Kwanaki Kafin Zabe A Iraki November 6, 2025 Araghchi : Yakin kwanaki 12 ya bamu babban darasi November 6, 2025 Putin : zamu dauki mataki idan Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
A yau Laraba 5 ga watan Nuwamba, an bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa (CIIE) karo na 8 a birnin Shanghai. A yayin wani taron manema labarai na yau da kullum da ya gudana a wannan rana, mai magana yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta nuna cewa, nasarar karbar bakuncin bikin baje kolin CIIE tsawon shekaru takwas a jere ta nuna kudurin kasar Sin da ayyukanta na cika alkawarinta na bude kofa, da kuma cimma burin samun moriyar juna da kuma nasara ga kowane bangare.
Mao Ning ta bayyana cewa bikin baje kolin na CIIE shi ne babban baje kolin kayayyaki a matakin na kasa na farko a duniya wanda ke da jigon shigo da kayayyaki daga waje, kuma wani sabon salo ne da yunkuri mai alfanu ga kasar Sin don ta fadada bude kofa ga sauran kasashe.
Girman bajen kolin CIIE na wannan shekarar ya gawurta zuwa sabon matsayi, inda kamfanoni sama da 4100 daga kasashen waje suke halarta. Harka tare da kasar Sin tamkar mabudi ne na samun damammaki, wanda hakan ya samu ittifakin amincewa a tsakanin dukkan bangarorin da suke halarta. Kasar Sin za ta ci gaba da fadada bude kofa da kuma sanya babbar kasuwarta ta zamo babbar dama ga duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA