Kotu ta yanke wa jagoran Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15
Published: 11th, September 2025 GMT
Wata babbar kotu a Abuja ta yanke wa Mahmud Muhammad Usman (Abu Bara’a), ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan kaso.
Abu Bara’a wanda Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta gurfanar a ranar Alhamis, ya amsa laifin gudanar da harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya ba shi damar mallakar makamai da aikata ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane.
Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin a ajiye Mahmud Usman a ofishin Hukumar DSS har zuwa lokacin da za a kammala shari’a kan sauran zarge-zargen da ake masa guda 31.
A lokacin gabatar da ƙarar, an tuhumi Mahmud Usman da Abubakar Abba da aikata ta’addanci a 2022, ta hanyar kai hari kan barikin soji ta Wawa da ke Ka’inji a ƙaramar hukumar Borgu ta Jihar Neja, lamarin da ya yi sanadiyar kisan mutane da dama.
Ana zargin su da koyon horo a kan sarrafa makamai da haɗa bama-bamai a sansanonin ’yan ta’ada da dama.
Mai Shari’a Nwite ya sanya ranar 21 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a ci gaba da shari’ar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ansaru
এছাড়াও পড়ুন:
Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
Sun jaddada cewa dole ne manyan kafafen sada zumunta su kare ‘yancin yin magana.
Sun kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya, ‘yan jarida, da masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama su tashi tsaye don hana abin da suka kira yunƙurin mayar da Nijeriya “mulkin kama-karya a intanet.”
Lamarin ya biyo bayan wa’adin sati guda da DSS ta bai wa Sowore da ya goge wasu wasu rubuce-rubuce game da Shugaba Bola Tinubu, wanda ya ƙi amincewa.
Hakan ya sa hukumar ta shigar da shi ƙara a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp