Dole ɗalibi ya kawo ‘Project’ ɗinsa kafin zuwa NYSC —Gwamnati
Published: 29th, September 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima (NYSC).
Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar.
Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka kammala karatu.
Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ya alaƙanta aikin Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da Tsarin Tattara Bayan Ilimi ma Kasa (NERD).
Ranar Laraba jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai dawo aiki Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba gyara titin Kano–Maiduguri baBisa haka, daga yanzu babu ɗalibin da za sahalewa zuwa NYSC ba tare da ya miƙa takardar shaidar kammala binciken karshe na kammala digirinsa ba.
Gwamnatin Tarayya ta ce hakan zai taimaka wajen yakar matsalar amfani da takardun kammala karatu na bogi da kuma adana ilimi da bincike a ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya Gwamnatin Tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Karamar Hukumar Dutse Sun Bukaci Gwamnatin Jigawa Ta Yashe Madatsar Ruwa Ta Warwade
Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin.
Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata.
Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum.
Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran bukatun yau da kullum.
Yace ana samun ribar kimanin naira dubu goma zuwa ashirin a kowace rana daga siyar da kifin ga matafiya da kuma baki masu kai ziyara garin.
A don haka, Umar yayi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta yi yashen madatsar ruwan saboda a samu karin kifaye da kuma ruwa da za a iya amfani da shi domin noman rani.
Shi ma a yayin tattaunawa da Dagacin Warwade, Malam Musa Ado, ya ce madatsar ruwan tana samar da ayyukan yi ga matasan yankin, tare da hana tafiya zuwa cirani a sauran yankunan kasar nan da sunan yin sana’o’i.
Ya ce matasan yankin suna gudanar da sana’ar kamun kifi da kuma nomar rani da ta damina.
Sai dai kuma, Malam Musa ya koka kan rashin samar da injinan noman rani da kuma Malaman gona kamar yadda ake yi a gwamnatocin baya.
Kazalika, yace a ‘yan kwanakin baya gwamnatin jihar Jigawa ta kai ziyara kauyen inda ta sanar da cewar Bankin duniya zai samar da wasu kudade ta hannun gwamnatin tarayya wanda za’a baiwa gwamnatocin jihohi domin yashewa tare da gina burtuloli da hanyoyin noman rani.
Bisa haka ne dagacin yayi kira ga gwamnatin jihar da ta fara yin garambawul a madatsar ruwan domin a baiwa mazauna yankunan damar amfani da shi.
A shekarun baya dai, gwamnatin jihar Jigawan ta samar da irin kifaye guda dubu Dari uku domin inganta samar da kifi a yankin.
Usman Mohammed Zaria