Aminiya:
2025-11-06@14:33:52 GMT

Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah

Published: 6th, November 2025 GMT

Wani sabon kudiri da ke gaban Majalisar Dokokin Amurka ya nemi a hana ’yan kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah da Miyetti Allah Kautal Hore bizar shiga Amurka.

Kudurin, wanda dan majalisa Christopher Smith ya gabatar a ranar Talata, ya kuma bukaci kwace kadarorin mambobin kungiyar.

An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa

Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin Amurka ke ɗauka don dakile abin da ta kira take hakkin ’yancin addini ga Kiristocin Najeriya.

Kudirin dai na neman hukunta mutane da ƙungiyoyi da ke da hannu ko goyon baya wajen take hakkin ’yancin addini mai, a ƙarƙashin dokar kasa da kasa ta IRFA.

Christopher ya yaba wa Shugaba Trump bisa sake ayyana Najeriya a matsayin Ƙasa Mai Ƙalubale Na Musamman, yana mai ambato rahotannin ci gaba da hare-hare kan al’ummomin Kirista a sassan ƙasar.

Kudirin ya kuma ambaci ’yan ta’adda Fulani da ke kai hare-hare a jihohin Binuwai da Filato a cikin kungiyoyin da ake sa’ido a kansu, wani matsayi da Amurka ke warewa ga ’yan ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba da ake zargi da take hakkin addini.

Sauran irin wadannan kungiyoyin da aka ayyana a baya a ƙarƙashin dokar sun haɗa da Boko Haram, ISWAP, ISIS-Sahel, Taliban da kuma Houthi.

Idan aka amince da kudirin, zai bai wa hukumomin Amurka damar hana biza da kuma kulle kadarorin mutanen da ke da alaƙa da waɗannan ƙungiyoyi.

An gabatar da kudirin ne bayan watanni na kiraye-kirayen yin hakan daga ’yan majalisar dokokin Amurka da ƙungiyoyin Kiristoci masu tsattsauran ra’ayin.

Shugaban Amurka Donald Trump dai ya yi zargin ana yi wa Kiristoci a Najeriya kisan kiya, amma gwamnatin kasar ta yi fatali da zarge-zargen inda ta kira shi a matsayin na karya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

DRC: Kungiyar M23 Ta Kafa Kotunanta A gundumar Kivu Ta Arewa

Kungiyar ‘yan tawayen M23 tare da hadin gwiwar kungiyar AFC sun kafa kotunan shari’a a cikin yankunan da suke iko da su a gundumar Kivu ta Arewa.

A garin Goma kungiyar ta sanar da kafa kotuna 378 a fadin yankunan da suke karkashin ikonta, lamarin da gwamnatin Kinshasha ta bayyana a matsyin haramtacce.

Wani makusancin kungiyoyin tawayen dake rike da yankunan gabashin DRF, Elie Mutela ya sanar da cewa; Tsarin mulkin kasar ya tabbatar da cewa bai kamata a bar mutane ba tare da tsarin shari’a ba, wannan ne dalilin da ya sa kungiyoyin M23/AFC su ka kafa kotuna domin yi wa mutane shari’a akan matsalolin yau da kullum.

Tun a ranar 14 ga watan Satumba ne dai aka fara farfado da tsarin shari’ar,tare da zabar alkalan da za su tafiyar da kotunan.

Wani mai rajin kare hakkin bil’adama a yankin Gueul Mamulaka ya ce; Labari ne mai dadi,amma kuma a lokaci daya mai cike da makaki.”

Ya kuma kara da cwa; Da akwai cin karo da juna a cikin abinda M23 take son yin a kafa kotuna da kuma yadda Kinshasha ta ce,hakan ba ya kan doka.

Gwamnatin Kinshasha ta yi tir da abinda kungiyar M23 take yi, tare da da cewa kotunan da za ta kafa ba su wani matsayi na shari’a.

Yankunan gabashin kasar DRC mai arzikin ma’adanai ya dade yana fama da rikice-rikice, da a halin yanzu kungiyar ‘yan tawaye ta M23 da abokan kawancenta suka shimfidi ikonsu a ciki.

Gwamnatin kinshasha dai tana zargin kasar Rwanda da cewa ita ce take goyon baya da taimakon kungiyar ta M23 da kuma ba ta makamai da sojoji.  Gwamnatin kasar Rwanda ta sha kore wannan zargin.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin  Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi  November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojin Amurka sun gabatar da shirin ƙaddamar da hari a Najeriya
  • Najeriya ta yi watsi da sanya sunanta cikin jerin kasashen da ake tauye ’yancin addini
  • DRC: Kungiyar M23 Ta Kafa Kotunanta A gundumar Kivu Ta Arewa
  • Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150
  • Ba addini ne kaɗai ke haifar da rikici a Nijeriya ba — EU
  • Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
  • Dalilin da Trump ya yi iƙirarin ana kisan Kiristoci a Nijeriya — Ndume
  • Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Ya Jaddada Gagarumin Tsaron Kasa Da Gwagwarmaya Ta Baiwa Lebanon
  • Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha