An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi
Published: 8th, November 2025 GMT
Sanarwar ta ce, “A ranar 2 ga Oktoba, 2025, misalin karfe 08:25 na safe, wani mutumin kirki ya kai rahoton kisan gilla a ofishin D Dibisional Police Headkuarters.
“Rahoton ya bayyana cewa wasu mutane biyu sun je gidan wani Ahmad Lawan, namiji, mai shekaru 29, wanda ake kira Soje, mazaunin Sabon Kasuwa, wanda ake zarginsa a matsayin shahararren dan sara-suka.
“Suka kwankwasa kofar gidansa, bayan da ya bude, sai suka soka masa wuka a kirji sannan suka tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba.”
Wakili ya bayyana cewa jami’an da ke karkashin D’ Dibision, karkashin jagorancin DPO CSP Mubarak Sani Baba, “sun hanzarta zuwa wurin da abin ya faru, suka dauki wanda abin ya shafa zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.”
Ya kara da cewa an mika gawar ga iyalansa domin a yi masa jana’iza bisa tsarin Musulunci.
A cewar binciken farko, ‘yansanda sun gano Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da Duduwa, da Abubakar Mohammed, a matsayin manyan masu hannu a kisan.
Bayan an binne Lawan, Wakil ya ce wasu fusatattun matasa sun kai farmakin ramuwar gayya inda suka kona gidan iyalin daya daga cikin wadanda ake zargi.
“Amma hadakar jami’an Rapid Response Skuad, Operation Restore Peace da D’ Dibision suka iso da gaggawa suka dakile rikicin,” in ji shi.
‘Yansanda sun kara bayyana cewa daya daga cikin manyan wadanda ake zargi, Abubakar Ibrahim (Duduwa), wanda ya fara tserewa, daga baya an gan shi yana yawo a Mararraban Liman-Katagum, kuma jami’an tsaro na sa-kai suka kama shi.
“Yayin da ake kai shi ofishin ‘yansanda, wasu fusatattun matasa suka tare su a Kwanar Kwaila suka kai masa hari da takubba, wanda ya jawo karaya a hannuwansa biyu da kuma mummunan rauni a kansa,” in ji Wakil.
Ya ce jami’an ‘yansanda sun iso da gaggawa inda suka ceci wanda ake zargin, suka tarwatsa matasan, sannan suka garzaya da shi ATBUTH domin jinya.
Sanarwar ta kara da cewa duk wadanda aka kama suna kan bincike domin tantance irin rawar da kowane dayansu ya taka a lamarin.
Wakil ya ruwaito Kwamishinan ‘Yansanda, CP Sani-Omolori Aliyu, yana gargadin iyaye da shugabannin al’umma da su ja kunnen ‘ya’yansu kada su bari a yi amfani da su wajen tayar da hankalin jama’a.
“Rundunar ba za ta yi wata-wata ba wajen daukar mataki mai tsauri kan duk wanda ko wata kungiya da gangan ta kawo tabarbarewar doka da oda ta kowace siga. Duk wanda aka kama da laifi za a hukunta shi bisa cikakkiyar doka,” in ji Aliyu.
Ya kara da cewa an tura tawagogin jami’an musamman a sassa daban-daban na jihar domin tabbatar da bin doka da oda yadda ya kamata.
A tuna cewa, kamar yadda jaridar PUNCH Metro ta ruwaito a 2024, rundunar ta taba kama wasu mutane makamantan wadannan bayan kisan gilla da aka yi wa wani Adamu Alkasim a unguwar Bayan Gari, Bauchi.
A lokacin, an kama mutum biyu Usman Shehu, mai shekara 20, da Abdullahi Abubakar, mai shekara 19, bisa zargin “hada baki wajen aikata laifi da kuma kisan kai.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita
Wasu fusatattun matasa a ƙauyen Sokupkpan da ke karamar hukumar Edu a jihar Kwara, sun kashe Babban Limamin yankin, Mallam Abdullahi Audu, bisa zargin shi da alhaki kan mutuwar wani matashi, Ibrahim Gana ta hanyar maita.
Shaidu sun ce lamarin da ya faru a ranar Laraba ya jefa al’ummar yankin cikin rudani da firgici.
Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a AbujaAn ce wannan farmakin ya samo asali ne daga zargin cewa limamin ya yi amfani da maita wajen cutar da mamacin.
A cewar majiyoyi, kafin rasuwarsa, Gana ya dade yana fama da wata cuta da ba a bayyana ba, kuma ya sha faɗa cewa Babban Limamin yana damunsa a mafarki.
An ce ya sha gaya wa abokai da danginsa cewa limamin ne ke haddasa tabarbarewar lafiyarsa ta hanyar sihiri.
“Yayin da lafiyarsa ke ƙara tabarbarewa, mutane suka fara yarda da zargin nasa. Da ya mutu, wasu matasa suka yanke shawarar cewa limamin ne ke da laifi,” in ji wata majiya daga yankin.
A ranar Laraba, rikici ya ƙara ƙamari yayin da ’yan uwan mamacin – Mohammed Shaba, Mamudu Gana, da Ndakpotun Issa, suka tara wasu matasa don tunkarar limamin.
Duk da ƙoƙarin wasu dattawa na kwantar da hankali, gungun matasan sun kai wa limamin hari, inda suka lakada masa duka har ya ce ga garinku nan.
“Sun afka wa limamin suna zarginsa da kashe Gana ta hanyar sihiri. Sun ƙi sauraron duk wanda ya yi ƙoƙarin dakatar da su,” in ji wata majiyar.
’Yan sanda daga ofishinsu na Tsaragi sun isa yankin bayan faruwar lamarin, inda suka kama wasu da ake zargi da jagorancin harin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, tana mai bayyana shi a matsayin “kisan gilla mai ban tsoro.”
Ta ce binciken farko ya nuna cewa bayan mutuwar Gana mai shekaru 25 a ranar 4 ga watan Nuwamba, ’yan uwansa Mohammed Shaba da Mahmud Gana sun zargi Babban Limamin da haddasa mutuwarsa, kuma suka tara wasu don kashe shi.
A cewarta, “An kama mutane huɗu, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran da suka shiga lamarin.”
Ta ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Adekimi Ojo, ya yi alla-wadai da lamarin, yana mai gargaɗin jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.
Tuni da aka yi jana’izar limamin bisa koyarwar addinin Musulunci.