Najeriya ta yi watsi da sanya sunanta cikin jerin kasashen da ake tauye ’yancin addini
Published: 6th, November 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da matakin da Gwamnatin Amurka ta dauka na sanya sunan Najeriya cikin jerin “Kasashen Da Ake Tauye ’Yancin Addini” , wato jerin kasashen da ake zargi da take hakkin addini.
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Mohammed Idris Malagi ne, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya ba ta shafi wani rukuni na addini ko kabila kai-tsaye ba.
Ya ce masu yada bayanan karya ne suka sa ake ganin kamar Najeriya tana nuna bambanci ta fuskar addini.
Malagi, ya ce gwamnati tana ci gaba da kokari wajen inganta harkar tsaro, sai dai ya bayyana cewa jami’an tsaro na wahala wajen isa wasu yankuna masu nisa a kan lokaci, don kai dauki.
Ya kara da cewa gwamnati na shirin dawo da tsarin tsaron al’umma domin tallafa wa rundunar tsaro ta kasa.
Da aka tambaye shi ko rashin nada jakadu ne ya haddasa wannan ce-ce-ku-ce da Amurka, Malagi ya ce dangantakar Najeriya da Amurka da sauran kasashe na tafiya daidai, kuma Shugaba Bola Tinubu na kokarin warware batun nada jakadu.
’Yan siyasar da suka fadi zabe ne ke yada labaran karya — AlakeA nasa bangaren, Ministan Harkokin Ma’adanai, Dele Alake, ya ce wasu ’yan siyasa da suka fadi a zabe ne ke yada labaran karya a Amurka cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya.
Ya gargade su da cewa irin wadannan maganganu na iya haddasa karin tashin hankali wanda zai iya shafar kowa, ba tare da la’akari da addini ba.
Keyamo ya karyata zarginShi ma Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce ikirarin Amurka karya ne, domin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta nuna wariyar addini.
Ya bayyana cewa yawancin manyan hafsoshin tsaro a Najeriya Kiristoci ne, sannan kuma Tinubu Musulmi ne matarsa Kirista, wacce malamar coci ce.
Keyamo, ya kara da cewa matsalolin tsaro a Najeriya suna shafar Musulmi da Kiristoci baki daya, don haka ya roki gwamnatin Amurka ta taimaka wajen yaki da ta’addanci maimakon dogaro da rahotannin karya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: labaran karya zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja
Bayan shafe lokaci, wani jami’in hukumar shige da fice ya dawo mata da fasfo ɗinta.
Duk da haka, Natasha ta ci gaba da nuna ɓacin ranta.
“Da ban yi bidiyon kai-tsaye ba, da ba za su dawo da min fasfo ba.”
A halin da ake ciki, ofishin Akpabio da Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ba su fitar da wata sanarwa ba game da lamarin.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA