Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba
Published: 5th, November 2025 GMT
Kungiyoyin agaji da dama na kasashen duniya sun yi gargadin cewa tallafin da ake bai wa yankin Gaza bai isa ba kusan wata guda bayan da aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da yankin ke ci gaba da fuskantar matsalar abinci da matsugunai yayin da hunturu ke gabatowa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ta nuna cewa rabin kayan abinci da ake bukata ne kawai ke isa yankin da aka killace.
Abeer Etefa, babban mai magana da yawun WFP, ya bayyana cewa hukumar ta isar da tan 20,000 na abinci, kusan rabin adadin da ake bukata, kuma ta bude wuraren rarraba abinci 44 daga cikin 145 da aka tsara.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin Jinkai (OCHA) a Falasdinu shi ma ya ba da rahoton cewa karancin mai, musamman iskar gas, yana kara ta’azzara rikicin, wanda ya tilasta wa sama da kashi 60% na mutanen Gaza su dafa abinci ta hanyar kona shara, wanda hakan ke haifar da babbar barazana ga lafiyar jama’a.
A ranar 10 ga Oktoba, tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani ya fara aiki a Zirin Gaza.
An yi wannan yarjejeniyar tsagaita wuta ne domin a samu kwararar kayan agaji zuwa yankin da ke da cunkoson jama’a, inda aka tabbatar da yunwa a watan Agusta, kuma kusan dukkan mazauna yankin miliyan 2.3 sun rasa gidajensu sakamakon hare-haren bama-bamai da Isra’ila ta kai musu.
A cewar kiyasin Majalisar Dinkin Duniya, kashi 81% na kayayyakin more rayuwa na Gaza sun lalace ko kuma sun ruguje.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu November 5, 2025 Ansarullah: Dakarunsu A Shirye Suke Don Tunkarar Duk Wata Barazana Daga Isra’ila November 5, 2025 Shugaban Najeriya Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU November 5, 2025 Kakakin Dakarun IRGC Ya Ce; Ko Kadan Amurka Ba Abar Amincewa Ba Ce November 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Turkiyye na karbar taron Kasashen Musulmi Kan Halin Da Ake Ciki A Gaza
Turkiyye na karbar bakuncin wani taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmi kan halin da ake ciki a Gaza.
Wannan taron ya zo ne bayan makonni uku da fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
A cewar Turkiyya, manufar taron ita ce taimakawa wajen mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sake tabbatar da rawar da take takawa a wannan batu.
Ƙasashen musulmin dake halartar taron na yau Litini a Istanbul su ne wadanda Donald Trump ya aminta dasu don tabbatar da nasarar shirin zaman lafiya na Gaza.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyye Hakan Fidan, wanda ke karbar bakuncin takwarorinsa, ya gabatar da wannan taron a matsayin hanyar yin nazari kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta, samar da matakai na gaba, da kuma daidaita su kafin tattaunawa da kasashen Yamma.
Haka kuma hanya ce ga wadannan kasashen da suka fi yawan al’ummar Musulmi su nuna jajircewarsu wajen kiyaye yarjejeniyar tsagaita wuta.
Ya bayyana tsagaita wuta a matsayin mafi rauni idan aka yi la’akari da kalubalen da mataki na biyu na shirin ke fuskanta.
Mataki na biyu na shirin na Trump ya tanadi kwance damarar makamai na kungiyar Hamas, samar da rundunar sulhu, da sauransu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza November 3, 2025 Girgizar kasa ta yi ajalin gomman mutane a Afghanistan November 3, 2025 Najeriya : tun kafin kalamman Trump muka dauki matakai November 3, 2025 Sudan : Mutane 1,500 sun rasa matsugunansu sakamakon tashin hankali November 3, 2025 UNICEF Tayi Gargadi Game Da Mawuyacin Hali Da Yara Ke Ciki A Gaza November 3, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Zargin Da Amurka Tayi Mata Kan Batun Motocin Agaji A Gaza November 3, 2025 El-Zakzaki: Yakin Sudan Yana Kare Maslahar Kasashen Yamma ne Kawai November 3, 2025 Iran Ta Karbi Sako Kan Batun Komawa Teburin Tattaunawa Ba Kai Tsaye Ba November 3, 2025 Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan: Mayakan RSF Sun Kashe Mata 300 Da Yi Wa 25 Fyade A El Fasher November 3, 2025 Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci