Iran da Pakistan sun habaka cinikayyar kan iyaka don karfafa alakokin kasuwanci da tsaro
Published: 9th, November 2025 GMT
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce faɗaɗa cinikayyar kan iyaka da hadin gwiwar tattalin arziki Tsakanin Iran da Pakistan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kuma habaka ci gaban kasashen biyu, yayin da ake kokarin samar da sabbin damammaki don ci moriyar juna a tsakaninsu.
Da yake magana bayan dawowarsa daga ziyarar kwanaki uku da ya kai Pakistan ranar Juma’a, ya ce, “Idan aka habaka kasuwannin kan iyaka kuma ciniki da Pakistan ya ci gaba da bunkasa, to za a magance yawancin matsalolin rashin tsaro da kalubalen kan iyaka tsakanin kasashen biyu, domin mayar da yankunan kan iyaka zuwa cibiyoyin manyan ayyukan tattalin arziki zai rage fasa-kwauri da rashin tsaro, haka nan kuma zai share fagen samun kwanciyar hankali da kuma amfanin juna.”
Tafiyar, wadda ta fara a ranar Laraba bisa gayyatar Kakakin Majalisar Dokokin kasar Pakistan Sardar Sadiq, ta hada da ganawa da manyan jami’ai kamar Mukaddashin Shugaban kasa kuma Shugaban Majalisar Dattawa Yusuf Raza Gilani, Firayim Minista Shehbaz Sharif, da Babban Hafsan Hafsoshin Soja Asim Munir.
Ya kara da cewa “daya daga cikin manyan manufofin wannan ziyarar ita ce nuna godiya ga jama’a da jami’an Pakistan saboda matsayins da suka dauka a lokacin yakin kwanaki 12 da gwamnatin Sahyoniya ta kaddamar kan Iran,” yana mai cewa duk inda tawagar Iran ta hadu da jama’a, suna nuna farin ciki game da martani mai karfi da Iran ta mayar ga zaluncin gwamnatin Sahyonya.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tanzania: ‘Yan sanda sun kama wani babban jigon adawar siyasa November 9, 2025 Martanin Iran ya haddasa wa Isra’ila hasarar fiye da Dala Miliyan 200 November 9, 2025 Biden Ya Caccaki Trump Bisa Tuhumarsa Da Kawo Barna November 9, 2025 Masar da Rasha sun tattauna batutuwan tsagaita wuta a Gaza da kuma Sudan November 9, 2025 Dan Wasan Taekwando Na Kasar Iran Abulfazl Zandi Ya Zamo Shi Ne Na Daya A Duniya November 8, 2025 Iraki Na Samun Zaman Lafiya Kuma Tana Kokarin Kawo Karshen Zaman Sojojin Ketare A Kasar November 8, 2025 Turkiya Ta Fitar Da Sammacin Kama Natanyaho Da Wasu Jami’ian Isra’ila Kan Yakin Gaza November 8, 2025 Shugaban Najeriya da takwaransa na kasar Saliyo Sun yi Ganawar Sirri a birnin Abuja November 8, 2025 Nigeria: Za A Ci Gaba Da Zaman Shari’ar Shugaban Kungiyar “IPOB” A ranar 20 Ga Watan Nan Na Nuwamba November 8, 2025 Ukraine: Fiye Da ‘Yan Afirka 1000 Ne Suke Taya Rasha Yaki Da Kasar Ukiraniya November 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas
An rantsar da Paul Biya mai shekaru 93 a matsayin shugaban kasar Kamaru karo na takwas a majalisar dokokin kasar da ke Yaoundé.
Ya shafe shekaru 43 yana mulki, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai.
Biya wanda shine shugaban kasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na kuri’un zabe, yayin da abokin hammayarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar kasa.
Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaben, yana zargin cewa an yi maguɗi,wanda hukumomi suka musanta. Lamarin dai ya janyo zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi.
Shugaban Kamaru Paul Biya ya yi alkawarin dawo da doka a kasar bayan tashin hankalin da aka samu bayan zabe.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar November 7, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jin Isra’ila . November 7, 2025 Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne November 7, 2025 Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar November 7, 2025 Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani November 6, 2025 Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu November 6, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza November 6, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku A Kudancin Lebanon November 6, 2025 Sayyid Muqtada al-Sadr Ya Fadakar Da Magoya Bayansa Kwanaki Kafin Zabe A Iraki November 6, 2025 Araghchi : Yakin kwanaki 12 ya bamu babban darasi November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci