Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150
Published: 5th, November 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da sabon shirinsa na ciyo sabon bashin Naira tiriliyan 1.150, don cike gibin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2025.
Buƙatar na kunshe ne cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisar na ranar Talata.
A cikin wasiƙar, Shugaba Tinubu ya ce za a samo bashin ne daga kasuwar bayar da lamuni ta cikin gida.
Ya ce buƙatar karbo bashin ta zama dole ne sakamakon ƙarin girman kasafin kuɗin shekarar 2025. Shugaban ya kuma ce an gabatar da buƙatar ne bisa tanadin Sashe na 44 (1) da (2) na Dokar Ƙarfafa Tattalin Arziki.
Bayan karanta wasiƙar, Akpabio ya mika buƙatar ga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da Na Waje domin ci gaba da nazari, tare da umarnin su kawo rahoto cikin mako guda.
Hakan dai na zuwa ne kwanaki shida kacal bayan Majalisar ta amince da buƙatar Tinubu ta karbo bashin dala biliyan 2.3 daga ketare, wanda shi ma za a yi amfani da shi don cike gibin kasafin kuɗin na 2025.
A cikin watanni huɗu da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kuma nemi amincewa da lamunin Dala miliyan 21.5 da Yen biliyan 15, tare da tallafin euro miliyan 65, a matsayin wani ɓangare na shirin lamunin waje na gwamnatin tarayya na shekarar 2025–2026.
Duk da ikirarin gwamnatin Tinubu na cewa samun kuɗaɗen shiga ya ƙaru tun bayan hawansa mulki, bashi ya ci gaba da zama hanyar cike gibin kasafin kuɗi.
A cewar Ofishin Kula da Basussuka na Najeriya (DMO), daga ranar 31 ga Disamba, 2024, jimillar bashin da Najeriya ke da shi ya kai naira tiriliyan 144.7 (kimanin dala biliyan 94.2).
Ƙaruwar bashin ta haifar da ƙarin kuɗaden da ake kashewa wajen biyan bashi. A shekarar 2023, Najeriya ta kashe naira tiriliyan 7.8 wajen biyan bashi, ƙari da kaso 121 cikin 100 idan aka kwatanta da naira tiriliyan 3.52 a shekarar da ta gabata.
A wata hira da manema labarai a watan Disamban bara, Shugaba Tinubu ya kare bukatarsa ta ciyo bashi, yana mai cewa ya ɗauki matakin ne ba don jefa ’yan Najeriya cikin wahala ba, sai don cika burinsa na inganta gine-gine da ababen more rayuwa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Ga Wani Dan Majalisa A Jihar Niger
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin dan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Agwara/Borgu a Jihar Neja, Honarabul Jafaru Mohammed Ali.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a jiya, a kauyen Kubul, kan hanyar Agwara zuwa Babana, a cikin Karamar Hukumar Borgu, yayin da dan majalisar ke hanyarsa ta zuwa ganawa da jama’arsa kan muhimmin shirin ci gaba.
Bayan harin, Honarabul Jafaru da tawagarsa sun samu rauni, inda aka garzaya da su asibiti, kuma suna karbar kulawar likitoci a halin yanzu.
A halin da ake ciki, jami’an tsaro sun isa yankin domin fatattakar ‘yan bindigar da kuma kare rayukan jama’a.
Duk da haka, babu wata sanarwa ta hukuma a hukumance a yanzu game da lamarin, sakamakon ci gaba da samun bayanai daga ma’aikatun tsaro.
Aliyu Lawal/Minna