An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita
Published: 6th, November 2025 GMT
Wasu fusatattun matasa a ƙauyen Sokupkpan da ke karamar hukumar Edu a jihar Kwara, sun kashe Babban Limamin yankin, Mallam Abdullahi Audu, bisa zargin shi da alhaki kan mutuwar wani matashi, Ibrahim Gana ta hanyar maita.
Shaidu sun ce lamarin da ya faru a ranar Laraba ya jefa al’ummar yankin cikin rudani da firgici.
An ce wannan farmakin ya samo asali ne daga zargin cewa limamin ya yi amfani da maita wajen cutar da mamacin.
A cewar majiyoyi, kafin rasuwarsa, Gana ya dade yana fama da wata cuta da ba a bayyana ba, kuma ya sha faɗa cewa Babban Limamin yana damunsa a mafarki.
An ce ya sha gaya wa abokai da danginsa cewa limamin ne ke haddasa tabarbarewar lafiyarsa ta hanyar sihiri.
“Yayin da lafiyarsa ke ƙara tabarbarewa, mutane suka fara yarda da zargin nasa. Da ya mutu, wasu matasa suka yanke shawarar cewa limamin ne ke da laifi,” in ji wata majiya daga yankin.
A ranar Laraba, rikici ya ƙara ƙamari yayin da ’yan uwan mamacin – Mohammed Shaba, Mamudu Gana, da Ndakpotun Issa, suka tara wasu matasa don tunkarar limamin.
Duk da ƙoƙarin wasu dattawa na kwantar da hankali, gungun matasan sun kai wa limamin hari, inda suka lakada masa duka har ya ce ga garinku nan.
“Sun afka wa limamin suna zarginsa da kashe Gana ta hanyar sihiri. Sun ƙi sauraron duk wanda ya yi ƙoƙarin dakatar da su,” in ji wata majiyar.
’Yan sanda daga ofishinsu na Tsaragi sun isa yankin bayan faruwar lamarin, inda suka kama wasu da ake zargi da jagorancin harin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, tana mai bayyana shi a matsayin “kisan gilla mai ban tsoro.”
Ta ce binciken farko ya nuna cewa bayan mutuwar Gana mai shekaru 25 a ranar 4 ga watan Nuwamba, ’yan uwansa Mohammed Shaba da Mahmud Gana sun zargi Babban Limamin da haddasa mutuwarsa, kuma suka tara wasu don kashe shi.
A cewarta, “An kama mutane huɗu, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran da suka shiga lamarin.”
Ta ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Adekimi Ojo, ya yi alla-wadai da lamarin, yana mai gargaɗin jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.
Tuni da aka yi jana’izar limamin bisa koyarwar addinin Musulunci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike
Ya ƙara da cewa yana cikin farin ciki ganin yadda Gwamna Douye Diri ya fice daga jam’iyyar, inda ya ce, “Shi da Makinde sun taɓa cewa ba za su bari a lalata PDP ba ko a jawo ta ƙasa, amma ga su yanzu; su ne suka faɗi ƙasa.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA