Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri
Published: 5th, November 2025 GMT
Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya mika motocin sintiri 63 ga hukumomin tsaro da kuma Rundunar Hadin Gwiwa ta Farar Hula (CJTF) da ke aiki a Maiduguri da kewaye.
Daga cikin motocin 63, an ba da motocin 30 ga sassa daban-daban na Sibiliyan JTF, 16 ga Jami’an tsaron kai daukin gaggawa don dakile masu aikata laifukan cin Zarafi, 10 ga kungiyoyin tsaro, 6 ga mafarauta da kuma daya ga jami’an Hukumar Kula da Fataucin Mutane (NAPTIP).
Rarraba motocin yana da nufin inganta karfin yin sintiri da mayar da martanin gaggawa musamman ga ‘yan sanda, sauran jami’an tsaro, da rundunar hadin gwiwa ta farar hula wajen magance barazanar tsaro kamar kungiyoyin ‘yan daba da sauran nau’ikan laifuka a cikin babban birnin jihar da kewaye.
Wannan gudummawar na daya daga cikin rarraba motocin da gwamnatin Zulum ta yi tun 2019, wadanda duk an yi niyya ne don karfafa tsarin tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da ci gaba da tallafawa jami’an tsaro.
Ya jaddada cewa tsaro wani vangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.
Ya ce, “muna nan a ci gaba da kokarinmu na tallafa wa jami’an tsaro a Jihar Borno da kayan aikin da ake bukata domin su yi aiki yadda ya kamata.
“Ina so in tabbatar muku da cewa gwamnatin Borno a karkashin jagorancina za ta ci gaba da tallafa muku da nufin cimma kyawawan manufofi na tabbatar da cewa jihar ta kawar da ta’addanci,” in ji gwamnan.
Zulum ya kuma yaba wa Shugaban Qasa Bola Ahmed Tinubu da jami’an tsaro kan kokarinsu na dawo da zaman lafiya a Borno.
Ya ce, “bari in yi amfani da wannan damar don mika godiyata ga Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Sojojin Nijeriya, Shugaba Bola Ahmed Tunibu da shugabannin ayyuka da Kwamandan Rundunar OPHK da kwamandojin sashe da dukkan jami’ai da ma’aikatan rundunar sojin Nijeriya da ke aiki don hada kan al’umma da kuma dukkan kungiyoyin ‘yan sanda a Jihar Borno saboda manyan ayyukan da suke yi a jihar.”
Taron ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Dakta Umar Usman Kadafur da Sakataren Gwamnatin Jihar Borno, Bukar Tijani da Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Borno, Naziru Abdulmajid da Daraktan Hukumar Tsaro ta Jiha, Adamu Umar da Kwamandan Rundunar Tsaron Farar Hula ta Nijeriya, Abdulrazak Haroon da sauran sassan Jami’an tsaro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jami an tsaro Jihar Borno
এছাড়াও পড়ুন:
‘YanSandan Jihar Kwara Sun Ceto Wasu Mutane Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara ta ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su ba tare da wata illa ba, a kauyen Igbonla.
A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi, ta fitar, ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin wani gida, suna harbi a sama, sannan suka tafi da wasu daga cikin mazauna gidan.
Daga nan ne rundunar ’yan sanda tare da ’yan banga da masu farauta suka isa yankin cikin gaggawa, lamarin da ya kai ga ceto sun hada da Fatima Wasiu da Kudus Wasiu da jaririya mai watanni shida, ba tare da jin rauni ba.
Sai dai har yanzu ana ci gaba da nemo sauran mutane biyu da aka yi garkuwa da su, wato Wasiu Salihu da Abdullahi Sefiu, kuma ana ci gaba da farautar wadanda suka aikata laifin.
Rundunar ta bukaci jama’a da su ci gaba da ba da bayanai cikin lokaci, domin sauƙaƙa aikin tabbatar da tsaro a jihar.
Ali Muhammad Rabiu/Kwara