Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe
Published: 7th, November 2025 GMT
A yau Juma’a ne dai masu shigar da kara a Tanzania su ka gabatar da tuhumar mutane da dama da zargin cin amanar kasa, saboda rawar da su ka taka a cikin rikicin zaben shugaban kasa.
Mutane 76 ne aka tuhuma da cewa; Sun yi kokarin kawo cikas akan zaben da aka yi a ranar 29 ga watan Oktoba da kuma tsokanar mahukunta a birnin Darussalam.
Baya ga laifin cin amanar kasa,ana kuma tuhumar mutanen da cewa sun kitsa aikata laifuka.
Zaben da aka yi a kasar Tanzani a karshen watan Oktoba, ya bar baya da kura saboda tashe-tashen hankulan da aka samu.
Babbar jam’iyyar adawa ta Chadema ta yi zargin cewa an kashe mutane fiye da 1,000,kuma a halin yanzu mahukuntan suna kokari boye duk wata shaida ta laifukan da su ka aikata ta hanyar binne gawawwaki a asirce.
Wadanda su ka sanya idanu a yadda aka gudanar da zaben sun ce, da akwai rashin gaskiya akan yadda aka gudanar da shi.
Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan wacce ta hau karagar Mulki a 2021 bayan rasuwar magabacinta, ta lashe zaben da kawo 97% kamar yadda mahukuntan kasar su ka sanar.
Manyan ‘yan hamayya a zaben shugaban kasar da su ne Tundu Lissu daga jam’iyyar Chadema, da luhaga Mpina na jam’iyyar ACT-Wazalendo, an hana su shiga zaben da aka gudanar. Tarayyar Afirka ta ce masu sa ido da ta aike sun bayyana mata cewa;zaben bai hau ma’auninta na inganci ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma November 7, 2025 Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan November 7, 2025 Tarayyar Turai: Ana Fuskantar Matsananciyar Wahalar Isar Da Kayan Agaji Zuwa Al-Fashar Na Sudan November 7, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon November 7, 2025 Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza November 7, 2025 Falasdinawa Miliyan 1.5 Ne Ke Cikin Mawuyacin Hali November 7, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Dage Takunkumi Kan Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Siriya November 7, 2025 Karuwar Matsalar Jin Kai Mafi Girma A Duniya A Sudan Saboda Ci Gaba Da Masifar Yaki A Kasar November 7, 2025 An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas November 7, 2025 Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar November 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya: Ta Sake Jaddada Yin Watsi Da Zargin Take Hakkin Kiristoci A Kasar
Gwamnatin Najeriya ta jaddada matsayinta na yin watsi da ayyata a matsayin kasa mai take hakkokin addinai da Amurka ta yi.
Da yake kare tarihin Najeriya, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa na Najeriya, Mohammed Idris, ya ce “barazanar Trump na ɗaukar matakin soja ba ta da tushe kuma hakan yana a matsayin kawar da ido ne daga ƙalubalen tsaro masu sarkakiya da Najeriya ke fuskanta,” ya ƙara da cewa “duk wani labari da ke nuna cewa Najeriya ta gaza ɗaukar mataki kan hare-haren da ake kai wa mabiya addini ya dogara ne akan bayanan ƙarya ko maganganu marasa tushe.”
A ranar Litinin, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Olufemi Oluwedi, ya bayyana cewa “Najeriya tana fuskantar ta’addanci, ba kai hari ko cin motuncin Kiristoci ba,” kuma “shugabancin Najeriya yana maraba da taimakon Amurka wajen yaƙi da ta’addanci matuƙar tana mutunta haƙƙinta na yankuna.”
Idris ya ƙara da cewa gwamnatinsu ta samu ci gaba mai yawa a yaƙi da ta’addanci tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023, yana mai cewa “kofar gwamnatin Najeriya ta kasance a buɗe kuma tana son yin aiki kafada da kafada da gwamnatin Amurka da sauran ƙasashe da abokan hulɗa don cimma burin kawar da ta’addanci gaba ɗaya a ƙasar Najeriya.”
Idris ya jaddada cewa “ta’addanci ya shafi Kiristoci da Musulmai,” kuma gwamnati ta kuduri aniyar kawo ƙarshen ayyukan masu tsattsauran ra’ayi ta hanyar ɗaukar matakan soja, haɗin gwiwa a yanki, da tattaunawa da abokan hulɗa na duniya.
A makon da ya gabata, Shugaban Amurka Donald Trump ya mayar da Najeriya cikin jerin ƙasashen da Amurka ta ce suna take ‘yancin addini. A ranar Asabar, ya ce ya umarci Ma’aikatar Tsaro da ta shirya don yiwuwar ɗaukar matakin soja cikin gaggawa idan Najeriya ba ta ɗauki mataki mai tsauri kan kisan Kiristoci ba. Matakin da Washington ta ɗauka ya kawo cikas ga dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gharibabadi: Kyakkyawar Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya Na Da Babban Tasiri Ga Yankin Da Ma Duniya November 6, 2025 Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba November 6, 2025 Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci