Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya
Published: 30th, September 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin soma karɓar haraji daga hannun mata masu zaman kansu waɗanda suka mayar da karuwanci sana’a.
Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kuɗi da gyaran dokokin haraji, Taiwo Oyedele, ya ce kuɗaɗen da masu sana’ar karuwanci ke samu za a riƙe cire musu haraji a ƙarƙashin sabuwar dokar haraji ta ƙasar.
Oyedele ya yi wannan bayani ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin X a jiya Litinin, inda ya kawo misalan hanyoyin samun kuɗin da ake sanya wa haraji.
Masanin harajin ya bayyana cewa sabbin dokokin ba su bambanta tsakanin hanyar halal ko ta haram wajen samun kuɗi ba — abin da suke dubawa kawai shi ne ko kuɗin ya fito daga cinikayyar haja ko kuma wani aiki da aka yi aka biya.
“Abu ɗaya game da dokar harajin shi ne ba ta bambance abin da aka yi halal ne ko akasin haka.
“Abin da take la’akari shi ne, shin kana samun kuɗi? Shin ka samu kuɗin ne ta hanyar aikin da kayi ko sayar da kaya? Idan haka ne, sai ka biya haraji.”
A gefe guda kuma, Oyedele ya ce kuɗaɗen tallafin gudanarwa ko ɗaukar nauyi da mutum zai aika wa ‘yan uwa, abokai ko ma baƙi ba a ɗaukar su a matsayin abin da ake cire musu haraji, domin ana ɗaukar su kyauta ce.
“Ka samu wani adadin kuɗi sannan ka aika wa ɗan uwanka, ko ma wani baƙo kuɗi a matsayin tallafi, ba komai ba ne.
“Idan kuɗin da kake aikawa na ɗaukar nauyi ne ko tallafi, ba don sun yi maka wani aiki ba, to wannan kyauta ce. Muna kiran shi mu’amala ba ta musayar wani abu ba. Wannan ba abin da za a cirewa haraji ba ne,” in ji Oyedele.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025
Manyan Labarai Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon November 17, 2025
Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025