An ceto ɗan ƙasar Masar da aka yi garkuwa da shi a Oyo
Published: 10th, September 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta sanar da ceto wani ɗan ƙasar Masar da wasu da ba a san ko su wane ba suka yi garkuwa da shi.
Kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Talatar nan a Ibadan, babban birnin jihar.
DSS ta warware tankiyar da ke tsakanin NUPENG da Dangote ’Yan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane 11 a ZamfaraYa ce an ceto ɗan Masar ɗin ne a ranar Talata da safe — kwana ɗaya kacal bayan sace shi — ba tare da an biya kuɗin fansa ba.
Osifeso ya ce an sace mutumin ne a yankin Alomaja, kusa da garin Idi-Ayunre, wani yanki da ke gefen birnin Ibadan.
A cewarsa, bayan samun rahoton garkuwar, sai Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Oyo, CP Femi Haruna, ya bayar da umarnin gaggawa ga sashen yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar.
Hakan ce ta sanya sashen ya haɗa gwiwa da rundunar ’yan sanda ta Jihar Ogun da kuma wasu mafarauta, inda suka shiga dazukan da ke tsakanin jihohin Oyo da Ogun domin kai farmaki.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, an yi saar gaske yayin da cikin awa 24 kacal, jami’an suka ceto ɗan ƙasar Masar daga hannun masu garkuwar.
Kakakin ’yan sandan ya ƙara da cewa yanzu haka an kai mutumin Asibitin Rundunar ’Yan Sanda na Eleyele da ke Ibadan domin duba lafiyarsa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS
Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi.
Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo na hudu ke nan a jere hauhawar farashin yana sauka.
NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murnaRahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar.
A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.
Ko alƙaluman da NBS ta fitar a watan Yuni, ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka zuwa kashi 22.22 daga 22.97 da aka samu a watan Mayu.
A baya dai dai an yi ta kiraye-kirayen gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan rage hauhawarar farashi domin magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.