Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba
Published: 6th, November 2025 GMT
Majalisar Tsaro ta Sudan ta ƙi amincewa da duk wani shirin tsagaita wuta, tana mai gindaya sharadin cewa sai dai idan (RSF) ta janye daga biranen da ta kwace iko da su.
Majalisar ta bayyana wannan matsayin ne a wani taro da aka gudanar a babban birnin Khartoum, don mayar da martani ga shawarar tsagaita wuta da Amurka ta gabatar.
A cewar majiyoyin, majalisar ta yanke shawarar ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana da kuma yin gangami don tunkarar abin da ta bayyana a matsayin “tawaye da makirci.” Majalisar ta kuma yi kira da a kafa sojojin sa kai na al’ummar kasa don tallafawa sojoji wajen tunkarar RSF.
Wata majiya ta shaida wa Al-Mayadeen cewa Sojojin Sudan suna yin gagarumin shirin yaki a bangarorin Kordofan da Darfur. Rahotanni sun ce sojoji sun yi watsi da tsagaita wuta har sai an sake kwace muhimman wurare daga hannun RSF.
Wani bayanin da ba a tabbatar da shi a hukumance ya yi nuni da cewa, Majalisar Tsaro ta Sudan, wacce shugaban Majalisar Mulkin Soja kuma shugaban rundunar sojojin Abdel Fattah al-Burhan ke jagoranta, za ta tattauna batun shirin tsagaita wuta da Amurka ta gabatar da nufin kawo karshen rikicin Sudan, a cewar wata majiya da ta tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran AFP.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya November 6, 2025 An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ribadu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya kan barazanar Trump
rahotanni suna nuna cewa mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya da jagororin sassan tattara bayanan sirri kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump.
Trump ya yi zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, inda ya ce yana so gwamnati ta dauki matakin gaggawa ko kuma ya turo sojoji domin su yaki maharan da ya bayyana da ƴanbindiga masu ikirarin jihadi.
A sanarwar, ya ce, “na ba sashen yaki umarni su fara shirin daukar mataki. Idan har za mu kai hari, to za mu kai harin ne cikin sauri ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda ƴan ta’addan nan suke kai hari kan kiristoci,” in ji shi, sannan ya kara kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi gaggawar daukar matakin magance matsalar.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta mayar da martani, inda shugaban kasar Bola Tinubu ya wallafa a shafinsa na kafofin sadarwa cewa babu wata barazana da kiristocin kasar suke fuskanta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon November 3, 2025 Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha November 3, 2025 An Sami Tsaikon Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Tanzania Saboda Rikicin Zabe November 3, 2025 Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Nablus Da Khalil November 3, 2025 Jagora: Sabanin Jamhuriyar Musulunci Da Amurka Daga Tushen Manufa Ne Ba Sama-sama Ba November 3, 2025 Turkiyye na karbar taron Kasashen Musulmi Kan Halin Da Ake Ciki A Gaza November 3, 2025 Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza November 3, 2025 Girgizar kasa ta yi ajalin gomman mutane a Afghanistan November 3, 2025 Najeriya : tun kafin kalamman Trump muka dauki matakai November 3, 2025 Sudan : Mutane 1,500 sun rasa matsugunansu sakamakon tashin hankali November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci