Aminiya:
2025-11-08@11:16:22 GMT

An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya

Published: 22nd, September 2025 GMT

Tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a Litinin ɗin nan a birnin Landan kamar yadda kafar labarai ta DW ta ruwaito.

Bikin ɗaga tutar na zuwa ne kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai

Shugaban tawagar jami’an diflomasiyyan Falasdinawa a Burtaniya Husam Zomlot, ya daga wani allo mai ɗauke da rubutun ‘Ofishin jakadancin Falasɗinu’ sannan kuma ya ce nan ba da jimawa ba za a buɗe ofishin a hukumance bayan kammala wasu sharudda dangane da dokoki da kuma tsarin gudanarwa.

Mista Zomlot ya yi jinjina ta musamman ga matakin Burtaniya na amincewa da kasar Falasɗinu da aka daɗe ana jira.

Ya ƙara da cewa yin hakan zai kawo ƙarshen zalunci na dogon lokaci, a daidai gabar da Falasɗinawa ke fuskantar matsananciyar wahala.

Birtaniya wadda ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila ta juya mata baya, sakamakon hare-haren da Isra’ilar take kai wa Zirin Gaza, wanda ya samo asali bayan da ƙungiyar Hamas ta kai wani mummunan hari a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Tun a watan Yulin wannan shekarar Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ce zai goyi kafa ƙasar Falasɗinu yana mai gindaya wa Isra’ilar sharaɗin yanke wannan shawarar.

A wancan lokacin Starmer ya ce zai amince da ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ilar ba ta ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas ba kafin babban taron Majalisar Dinkin Duniya na watan Satumba.

Sai dai a ranar Lahadi, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya zargi ƙasashen da suka sanar da aniyar amincewa da ƙasar Falasɗinu a matsayin masu ƙarkafa wa ta’addanci gwiwa.

Haka kuma, Netanyahu ya sake nanata cewa muradin samar da ƙasar Falasɗinu ba zai taba cika ba, tare da yin barazanar faɗaɗa mamayar Gabar Yamma da Kogin Jordan.

A yayin da Birtaniya, Australia da kuma Canada suka bi sabun sauran ƙasashen duniya sama da 140 domin amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ’yanci, a nahiyar Afirka kuwa, yanzu haka ƙasashe 52 daga cikin 54 ne suka amince da wannan ’yanci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Birtaniya ƙasar Falasɗinu

এছাড়াও পড়ুন:

Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia

’Yan sanda a kasar Indonesia sun ce an garzaya da daruruwan mutane zuwa asibiti bayan wani abu da ake zargin bam ne ya fashe a wani masallacin Juma’a da ke Jakarta babban birnin kasar.

Lamarin ya faru ne a lokacin sallar Juma’a a cikin wani ginin makaranta da ke Kelapa Gading, a arewaci Jakarta.

Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800

Kwamishinan ’yan sandan birnin, Asep Edi Suheri, ya ce har yanzu ana bincike don gano musabbabin fashewar.

Shaidun gani da ido sun ce sun ji fashewa biyu masu ƙarfi da misalin ƙarfe 12 na rana a agogon kasar, daidai lokacin da aka fara hudubar sallar Juma’a a masallacin.

Suheri ya ce an kai mutane 54, galibinsu ɗalibai zuwa asibiti da raunuka masu sauƙi da masu tsanani, ciki har da wadanda suka kone.

Ya ƙara da cewa mutum 20 na ci gaba da samun kulawa a asibiti, inda uku daga cikinsu ke fama da raunuka masu tsanani.

Suheri ya ce ƙungiyar ƙwararrun masu binciken bama-bamai da aka tura wurin ta gano bindigogin wasa da ƙaramar bindiga ta wasa a kusa da masallacin.

“’Yan sanda na ci gaba da binciken wurin don gano musabbabin fashewar,” in ji shi.

Kafafen yaɗa labarai na cikin gida a kasar sun nuna bidiyon da ke nuna layin ’yan sanda da ke kewaye da makarantar, inda motoci masu ɗaukar marasa lafiya ke tsaye a gefe.

Sai dai hotunan masallacin ba su nuna wata mummunar lalacewa ba sakamakon harin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja
  • Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila
  • An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi
  • Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna
  • Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia
  • An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8
  • Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
  • Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja
  • Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano
  • Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE