An kama mace ɗauke da bindiga da N2m a otal
Published: 5th, September 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Kogi ta kama wata budurwa mai suna Charity Williams ’yar shekaru 23, wadda aka same ta da kuɗi Naira miliyan 2,047.500 da miyagun ƙwayoyi da kuma bindigar fistol.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jami’anta da ke aiki da sashin Okene a Ƙaramar hukumar Okene a jihar, sun kama wanda ake zargin a wani otal da ke Okene.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar (PPRO), William Aya, ya ce bayan da aka samu labarin, jami’ansu sun kai farmaki otal ɗin tare da kama matar.
Aya ta ce babban wanda ake zargin kan lamarin wani ne mai suna Christopher Kadiri da ya tsere.
“A wani samame da jami’an tsaro na rundunar ’yan sandan Najeriya reshen Okene suka kai, sun kama Charity Williams, mai shekara 23, tare da ƙwato bindiga ƙirar fistol guda ɗaya, da kuɗi Naira miliyan 2,047,300 da harsashi na nau’in 9mm guda shida, muggan ƙwayoyi, gatari da wayoyin salula huɗu.
“Wannan ya biyo bayan bayanan sirri na cewa, an ga wani da ake zargi da aikata laifi a Yuwander Lodge a maɓoyar masu aikata laifi ne a ƙauyen Oguda, Okene.
“Nan take ’yan sanda suka kutsa kai cikin masaukin, bayan da suka binciki ɗaya daga cikin ɗakunan da wani Christopher Christopher Kadiri ya nema, wata mace mai suna Charity Williams mai shekara 23, an kama su kuma an ƙwato abubuwan da ke zargi a ɗakin,” in ji sanarwar.
Ya ce, ana ci gaba da ƙoƙarin cafke duk waɗanda ake zargin gaba ɗaya, yayin da ake ci gaba da bincike.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East.
A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp