Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku
Published: 8th, November 2025 GMT
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka November 7, 2025
Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi November 7, 2025
Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil November 7, 2025
এছাড়াও পড়ুন:
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
A gaskiya wannan yanayi ya yi matukar burge ni, kuma sai na zaci ko don saboda ina bako ne, amma yayin da na ga wasu Sinawa suna daukar hotunan bishiyoyin, sai na ce to, babu makawa wannan yanayi ne mai burge kowa da kowa, bako da dan gari kuma ciki har da dattawa. Nan take ni ma na zaro wayata, muka ci gaba da kashe hotuna ni da abokin aikina. Na yi kokarin nuna kawaici a kan yadda yanayin ya shaukantar da ni, amma sai na ga abokin nawa ya fi ni “jazabancewa”, domin shi ya fi ni yawan yin “style” na daukar hoton da kuma yawan hotunan da muka dauka.
Wani abu da na lura da shi a kasar Sin shi ne, ba kawai a manyan birane ba, hatta a garuruwa na gundumomi, kasar ta samar da lambuna masu furanni da koramu da itatuwa masu ban sha’awa, inda iyalai suke zuwa domin shakatawa musamman da maraice bayan tasowa daga makaranta.
Ni dai, idan wani mai yawon shaktawa ya tambaye ni, wane lokaci ne mafi dacewa ya kawo ziyara kasar Sin, zan ce masa ka zo a lokacin “yanayi mai launin zinare”, watau a lokacin kaka, musamman daga karshen watan Oktoba kafin shiga yanayin hunturu sosai lokacin da wannan launi zai sauya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA