Masu Sa Ido na Tarayyar Afirka: Zaben Tanzania Ya Keta Ka’idojin Demokradiyya
Published: 6th, November 2025 GMT
Tawagar masu sa ido ta Tarayyar Afirka ta sanar a ranar Laraba cewa zaɓen Tanzania “bai cika ƙa’idodin dimokraɗiyya ba,” tana mai tsokaci kan zaɓen da aka yi jayayya a kansa wanda ya haifar da zanga-zanga mai tsanani kwanan nan.
An ayyana Shugaba Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaɓen da gagarumin rinjaye a zaɓen da aka gudanar a ranar 29 ga Oktoba, amma ‘yan adawa sun zargi gwamnati da yin magudi a zaɓen, kuma zanga-zangar ta ɓarke bayan da aka soke manyan abokan hamayyarta.
Tawagar ta ƙara da cewa “a wannan matakin farko, tawagar ta kammala da cewa babban zaɓen 2025 a Tanzania bai yi daidai da ƙa’idodin Tarayyar Afirka da tsarin ƙa’idoji na kasa da kasa da kuma sauran alkawuran ƙasa da ƙasa na zaɓen dimokraɗiyya ba.”
Ta ƙara da cewa “masu sa ido sun lura da cunkoson jama’a a akwatuna a rumfunan zaɓe da dama, inda aka raba ƙuri’u da yawa,” sannan ta lura da “rashin wakilcin sauran jam’iyyun siyasa, haka nan kuma a lokacin ƙidayar ƙuri’a, an nemi wasu masu sa ido su bar rumfunan zaɓe.
Tawagar ta kara da cewa “Dole ne Tanzania ta ba da fifiko ga gyare-gyaren zaɓe da na siyasa don magance ƙalubalen dimokuraɗiyya a kasar.
A nata ɓangaren, gwamnati ta dage a kan cewa zaɓen ya gudane a cikin aminci da sahihanci da gaskiya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bisa Tuhumar Fitar Da Bayanai Na Hukuma November 5, 2025 Sudan Ta Sake Jaddada Tuhumar Kasar UAE Da Taimakon Rundunar RSF November 5, 2025 Shugaban Mali Ya Yi jawabi Akan Hana Shigar Da Man Futur Da Masu Ikirarin Jihadi Suke Yi November 5, 2025 Iran : bisa sharadi ne muka saki ‘yan Faransa daga gidan yari November 5, 2025 Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba
Kungiyoyin agaji da dama na kasashen duniya sun yi gargadin cewa tallafin da ake bai wa yankin Gaza bai isa ba kusan wata guda bayan da aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da yankin ke ci gaba da fuskantar matsalar abinci da matsugunai yayin da hunturu ke gabatowa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ta nuna cewa rabin kayan abinci da ake bukata ne kawai ke isa yankin da aka killace.
Abeer Etefa, babban mai magana da yawun WFP, ya bayyana cewa hukumar ta isar da tan 20,000 na abinci, kusan rabin adadin da ake bukata, kuma ta bude wuraren rarraba abinci 44 daga cikin 145 da aka tsara.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin Jinkai (OCHA) a Falasdinu shi ma ya ba da rahoton cewa karancin mai, musamman iskar gas, yana kara ta’azzara rikicin, wanda ya tilasta wa sama da kashi 60% na mutanen Gaza su dafa abinci ta hanyar kona shara, wanda hakan ke haifar da babbar barazana ga lafiyar jama’a.
A ranar 10 ga Oktoba, tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani ya fara aiki a Zirin Gaza.
An yi wannan yarjejeniyar tsagaita wuta ne domin a samu kwararar kayan agaji zuwa yankin da ke da cunkoson jama’a, inda aka tabbatar da yunwa a watan Agusta, kuma kusan dukkan mazauna yankin miliyan 2.3 sun rasa gidajensu sakamakon hare-haren bama-bamai da Isra’ila ta kai musu.
A cewar kiyasin Majalisar Dinkin Duniya, kashi 81% na kayayyakin more rayuwa na Gaza sun lalace ko kuma sun ruguje.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu November 5, 2025 Ansarullah: Dakarunsu A Shirye Suke Don Tunkarar Duk Wata Barazana Daga Isra’ila November 5, 2025 Shugaban Najeriya Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU November 5, 2025 Kakakin Dakarun IRGC Ya Ce; Ko Kadan Amurka Ba Abar Amincewa Ba Ce November 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci