Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya
Published: 8th, November 2025 GMT
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya nemi Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar da ya yi wa Najeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Najeriya saboda zargin ana zaluntar Kiristoci.
Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso RockBarau ya ce maganar da Trump ya yi ba ta dace ba, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Juma’a, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya ce Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba za ta yadda a ci zarafinta ko a tsangwame ta ba.
“Shugaban Amurka ya fito ya ce, ‘Najeriya wulaƙantaciyyar ƙasa ce, za mu kai muku hari,’ wannan bai dace ba.
“Ya kamata ya janye wannan maganar ya kuma nemi afuwar Najeriya,” in ji Barau.
Ya ƙara da cewa maganganun Trump sun karya dokokin diflomasiyya da na ƙasa da ƙasa.
“Idan kuna da ƙorafi a kan ƙasarmu, ku bi hanyoyin shari’a. Ku je Majalisar Ɗinkin Duniya, ku nemi izini, sannan ku aiwatar da shi yadda ya dace. Tsallake wannan hanya ba abin da ya dace ba ne,” in ji shi.
Barau, ya jaddada cewa kalaman Trump ba za su firgita Najeriya ba, kuma ya kamata shugaban Amurka ya girmama ƙasa mai cin gashin kanta.
“Ba za mu ji tsoron faɗin gaskiya ba. Da Trump yana nan, da na faɗa masa kai-tsaye cewa abin da yake yi ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa kuma ba daidai ba ne,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Barazana hari Sanata Barau zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta samu ci gaba sosai wajen magance matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar cikin shekaru biyu da suka gabata.
Shugaban ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na daƙile ayyukan ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiyar ƙasa.
Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masaiA wata sanarwa da Tinubu ya fitar a shafinsa na sada zumunta, a ranar Juma’a, ya ce ƙalubalen tsaro a Najeriya, da suka haɗa da ta’addanci da aikata laifuka, ana magance su da sabbin tsari da sauye-sauyen dabarun dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
“Haƙiƙa muna fuskantar ta’addanci – ƙalubalen da Najeriya ta fuskanta kusan shekaru ashirin, kuma ba za mu ja da baya ba, za mu yi nasara a kan ta’addanci kuma mu yi iƙirarin samun nasara a wannan yaƙin, ba za mu taɓa yin sulhu harkar tsaro ba.
“Najeriya ƙasa ɗaya ce mai haɗin kai, mun tashi tare, mun ci gaba tare, kuma mun ƙi yanke ƙauna domin tabbatar da ƙuduri.
“Aikin da ke gabanmu yana da yawa, amma duk da haka ƙudurinmu ya fi girma, za mu ci gaba da ɗorewa tare da inganta nasarorin da muka samu na sake fasalin ƙasa da kuma samar da ci gaba a Najeriya.
“Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba kuma ba za mu bar wani abu ba a cikin aikinmu na kawar da masu aikata laifuka a cikin al’ummarmu, muna kira ga abokan haɗin gwiwarmu da su tsaya tsayin daka tare da mu yayin da muke ƙara faɗaɗa yaƙin da muke yi da ta’addanci, mun samu gagarumin ci gaba a cikin shekaru biyu da suka gabata, kuma za mu kawar da wannan barazana.”