Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano
Published: 5th, November 2025 GMT
Ana fargabar cewa wasu yara biyu sun riga mu gidan gaskiya bayan faɗawa rijiya a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Dala da ke Jihar Kano.
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan TinubuA cewarsa, tsautsayin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 8:53 na safiyar ranar Talata a ƙauyen Kashirmo da ke yankin Sarkakiya na Dawakin Tofa, inda wata yarinya mai shekara takwas mai suna Zara’u Muhammad ta faɗa wata rijiya da ke kusa da gidansu.
Duk da ƙoƙarin jama’a na ceto yarinyar kafin isowar jami’an hukumar kashe gobara ya ci tura, saboda zurfin rijiyar da kuma yawan ruwan da ke cikinta.
Sai dai daga bisani an tsamo gawarta, sannan aka miƙa ta ga dagacin yankin, Abdullahi Garba.
Sai kuma a Larabar ce makamancin wannan lamari ya auku, inda wani yaro mai shekara shida, Ahmad Abdurashid, ya faɗa rijiya a unguwar Dandishe Tsamiyar Goodluck da ke a ƙaramar hukumar Dala.
An dai samu nasarar ceto yaron a raye amma daga bisani ya ce ga garinku nan.
Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas, ya bayyana baƙin ciki kan faruwar irin waɗannan lamurra, yana mai roƙon jama’a da su riƙa rufe rijiyoyi da kyau da kuma kula da yara ƙanana domin guje wa irin wannan mummunan sakamako.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano rijiya yara
এছাড়াও পড়ুন:
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a Tanzaniya
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya.
A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba.
An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — TrumpRiƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.”
Baƙin da aka gayyata ne kawai aka bai wa damar halartar rantsar da Shugaba Hassan a bikin da aka haska duk da katse intanet, yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar kan sakamakon zaɓen.
An ayyana Hassan, wadda ta hau mulki a shekarar 2021 bayan rasuwar tsohon shugabanta, a matsayin wadda ta lashe zaɓen Larabar makon da ya gabata da kashi 97.66% na ƙuri’un da aka kaɗa.
Sai dai ’yan hamayya sun yi watsi da sakamakon kan zargin maguɗi, suna mai cewar an yi amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima kan masu bore bayan ɓarkewar zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓen.
Hassan, mai shekaru 65, ta tsaya takara ne kawai da ’yan takara daga ƙananan jam’iyyu bayan da aka hana manyan masu ƙalubalantarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu shiga takarar.