Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-09-24@08:37:38 GMT

CORET Ta Yaba Da Nasarar Shirin Ciyarda Daliban Makarantun Makiyaya

Published: 22nd, September 2025 GMT

CORET Ta Yaba Da Nasarar Shirin Ciyarda Daliban Makarantun Makiyaya

 

Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan ɗalibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da ɗalibai.

 

Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Kaduna domin ƙara wa ma’aikata da abokan hulɗarsu ƙwarewa kan harkar ciyar da ɗalibai.

 

Taron ya mayar da hankali ne wajen duba nasarorin da aka samu cikin watanni goma tun lokacin da aka fara shirin a Ladduga, Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, da kuma Maigatari a Jihar Jigawa.

 

Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana cewa shirin ya shafi makarantun makiyaya kawai a jihohin Jigawa da Kaduna.

 

Ya ce ciyarwa na daga cikin manyan matsalolin da ke sa yara barin makarantu, don haka shirin ya ƙunshi amfani da al’ummomin yankuna wajen samar da abincin ɗalibai.

 

Ya ƙara da cewa an sayi kayan abinci daga cikin al’umma tare da haɗa su wajen tabbatar da ingancin abincin da ɗalibai ke ci. Bugu da ƙari, CORET ta samar da rijiyoyin burtsatse domin tabbatar da samun ruwa na sha da na yau da kullum.

 

Muhammed Bello Tukur ya yaba da irin goyon bayan da abokan hulɗa musamman ECOWAS, da kuma Gwamnatin Tarayya da Jihohi ke bayarwa wajen tabbatar da nasarar shirin.

 

A nasa jawabin, Ko’odinatan Shirin, Dakta Abdu Umar Ardo, ya bayyana cewa shirin ya zama nasara daga komai zuwa abu mai amfani tun da jihohin suka rungumi karatun ’ya’yan makiyaya.

 

Haka kuma, a kasidarsa, Bashir Abbo ya bayyana cewa bincike ya nuna akwai bukatar ƙwararrun malamai, farfaɗo da kwamitocin gudanar da makarantu da ƙarfafa ƙungiyoyin mata domin su riƙa taka rawar da ta dace.

 

Ya ce ɗaukar ƙarin malamai ƙwararru zai samar da sakamako mai kyau nan gaba.

 

Mahalarta taron sun fito ne daga Ladduga, yayin da wasu daga cikin mahalarta daga Karamar Hukumar Maigatari ta Jihar Jigawa suka halarci taron ta yanar gizo.

COV: Adamu Yusuf

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Masana Sun Yaba Da Shawarar GGI Da Kasar Sin Ta Gabatar A Taron Kara Wa Juna Sani Na CMG 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An yi wa sojoji ɗaurin rai da rai kan sayar wa ’yan ta’adda makamai a Borno
  • CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100
  • DSS ta yi wa Malami tambayoyi kan harin da aka kai masa a Kebbi
  • Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja
  • Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano
  • An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin tsaro a Kwara
  • Masana Sun Yaba Da Shawarar GGI Da Kasar Sin Ta Gabatar A Taron Kara Wa Juna Sani Na CMG 
  • Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Bayyana Ra’ayin Kasar Kan Rikicin Falasdinu Da Isra’ila
  • Gwamna Lawal Ya Raba Kayan Karatu 408,137 Ga Makarantun Gwamnatin Zamfara