Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (2)
Published: 19th, September 2025 GMT
Sai yace “A’a ba haram ba ne, kawai dai mutanena ba su san shi ba ne.” Annabi (SAW) ya taɓa cewa kar a ci tafarnuwa a shigo masallaci, aka tambaye shi: “Ya Rasulallah haram ne?” Sai ya ce “A’a ba na haramta abin da Allah bai haramta ba, kawai dai ni ne ba na son shi”, ka ga bambancin ladabin malamai na wancan zamani da na yanzu, a yanzu duk abin da wani Malami ba ya so sai kawai ya haramta shi.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ma’aikin Allah ne, Annabin Allah ne, sannan kuma shugaban ƙasa ne a wancan lokacin, shi yake tsara dokokin ƙasa (constitution) na ƙasarsa (Sallallahu Alaihi Wasallam), don haka yana hana wasu abubuwan kuma ya halatta wasu abubuwan, kamar yanda aka taɓa tambayar Abdullahi ɗan Abbas, sai ya ce: “to wallahi ni ma doka kaza da kaza ban sani ba na wucingadi ne ko kuwa na dindindin ne”. Don haka, majalisar dokoki ba za ta ce “na haramta kaza” ba, sai dai ta ce “na hana kaza saboda dalili kaza”, to duk ranar da wannan dalilin ya ɗauke sai ka ji an janye wannan hanin kuma.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam shari’arsa ta zo a mai tafiya ce, shi cikamakon Ma’aika ne, cikamakon Annabawa ne, don haka komai nasa na har ƙarshen halitta ne, don haka ne ya zamo rahama ga halitta gaba ɗaya. Don haka babu wanda za ka je masa da faɗa ka tilasta masa ya karɓi ra’ayinka, Manzo ne, Ma’aiki ne ga duk duniya gaba ɗaya, ya zo ya daidaita addininsa a cikinmu, ya yaɗa zaman lafiya a cikinmu, ya yaɗa girmama ɗan Adam; dama abu biyu ne addini; Allah ya saka ma Shehu Ibrahim (RTA) da alheri, yana cewa: “abu biyu ne addini, Girmama Allah da tausayin ɗan Adam, wannan shine addini”, duk abin da za ka ga addini yana kira, za ka ga a kan waɗannan abubuwan biyun ne. Don haka suka ce: “duk addinin da ya kira ka zuwa cewa kar ka tausaya ma ɗan Adam to ba daga Allah yake ba”. Domin Allah shi ya halicci ɗan Adam ɗin nan, shi ya busa masa ransa, to kuwa Allah Tabaraka wa Ta’ala ba zai wulaƙanta ɗan Adam ɗin nan ba.
Mutum kansa idan ya ƙera tukwane, ba zai yadda haka kawai wani ya zo ya farfasa masa tukwanensa ba, haka idan ka sayi sabon abin hawa ba zaka yarda kawai wani ya zo ya farfasa maka shi ba, da yara sun zo suna wasan jifa a kusa da abin hawan ka zaka kore su ne, ba don kar su fasa maka kai ba ne, a’a, domin kar su fasa maka abin hawan nan naka, to ka ga ta yaya Allah shi kuwa zai bar halittarsa a zo ana aibata ta ana halaka ta? Wallahi mu ji tsoron Allah. Wannan ya jawo ake mayar da addininmu baya. Manzon Allah ya zo ya yaɗa zaman lafiya, ya yaɗa girmama ɗan Adam, ya yaɗa soyayya a tsakaninsu, ya yaɗa daidaito a tsakanin ƙabilu da jinsunan mu, ayar Alƙur’ani ta ce, “Ya ayyuhan nasu innaa khalaƙnakum min zakarin wa untha, wa ja’alnaakum shu’uban wa ƙaba’ila lita’arafu; inna akramakum indallahi atƙaakum”. Ma’anar wannan aya ta sama tana nufin ko da Bayahude ko Bamajuse ko kuma ɗan kowanne addini idan ya fi ka tsoron Allah, to fa ya fika a wajen Allah, domin Allah “ya ayyuhan nasu” ya ce ba “ya ayyuhal muslimuna” ba.
Akwai wani Bature, ya karanta littafan Annabawa da suka gabata da duk sauran littafan da ake cewa Allah ne ya saukar dasu, ya dudduba ya yi nazari, sai da Allah ya kawo shi Misra, ya haɗu da abokinsa sai ya sami ganin Kur’ani ta wajen abokin nan nasa kuma abokin ya tabbatar masa cewa shi ma wannan littafi daga Allah ne, sai ya ce to a ba shi ya duba (watau Alkur’ani mai fassara zuwa Ingilishi). Yana fara karantawa sai kuwa ya ce: “Haba! Yanzu na ji Allah ne yake magana! Amma duk waɗancan sauran littafan ina jin wani mutum ne abokina ko wani sarki mutum ne yake magana!”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yadda Jama’a Ribas Ta Yi Cikar Ƙwari Yayin Da Gwamna Fubara Ya Koma Ofis
A lokacin dokar ta-ɓaci, Tinubu ya naɗa tsohon Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai yi mulki na rikon ƙwarya.
A jawabin bankwana da ya yi da safiyar ranar Alhamis, Ibas ya roƙi ’yan siyasa a jihar su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai da gwamnatinsa ta samar a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp