Aminiya:
2025-11-09@19:40:10 GMT

Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi

Published: 9th, November 2025 GMT

’Yan ta’addan Lakurawa sun kai hari sansanin Hukumar Kwastam da ke Maje, a Ƙaramar Hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi, inda suka kashe wani jami’i guda ɗaya.

Wani mazaunin yankin ya ce ’yan ta’addan sun zo da yawa, inda suka fara harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, sannan suka ƙone sansanin jami’an kwastam.

Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC

Ya ce, “Lakurawa sun zo da yawa, suna harbe-harbe ta ko ina.

Sun ƙone sansanin kwastam tare da kashe wani jami’i.”

Mai magana da yawun hukumar Kwastam a Jihar Kebbi, Muhammad Tajudeen, ya tabbatar da faruwar harin.

Ya ce jami’an hukumar suna asibiti suna jiran rahoton likita don tabbatar da ko jami’in da aka harba ya rasu.

Ya ce: “Harin ya faru da gaske, amma likita ne zai tabbatar ko jami’in ya rasu ko akasin haka. Muna jiran rahoton likita kafin mu fitar da cikakken bayani.”

Wannan harin na zuwa ne mako guda bayan wasu ’yan ta’adda sun sace mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Muhammad Sama’ila Bagudo.

Mazauna yankin sun bayyana cewa harin ya yi sanadin lalacewar kayayyakin kwastam a sansanin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hari Kwastam Lakurawa

এছাড়াও পড়ুন:

Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia

’Yan sanda a kasar Indonesia sun ce an garzaya da daruruwan mutane zuwa asibiti bayan wani abu da ake zargin bam ne ya fashe a wani masallacin Juma’a da ke Jakarta babban birnin kasar.

Lamarin ya faru ne a lokacin sallar Juma’a a cikin wani ginin makaranta da ke Kelapa Gading, a arewaci Jakarta.

Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800

Kwamishinan ’yan sandan birnin, Asep Edi Suheri, ya ce har yanzu ana bincike don gano musabbabin fashewar.

Shaidun gani da ido sun ce sun ji fashewa biyu masu ƙarfi da misalin ƙarfe 12 na rana a agogon kasar, daidai lokacin da aka fara hudubar sallar Juma’a a masallacin.

Suheri ya ce an kai mutane 54, galibinsu ɗalibai zuwa asibiti da raunuka masu sauƙi da masu tsanani, ciki har da wadanda suka kone.

Ya ƙara da cewa mutum 20 na ci gaba da samun kulawa a asibiti, inda uku daga cikinsu ke fama da raunuka masu tsanani.

Suheri ya ce ƙungiyar ƙwararrun masu binciken bama-bamai da aka tura wurin ta gano bindigogin wasa da ƙaramar bindiga ta wasa a kusa da masallacin.

“’Yan sanda na ci gaba da binciken wurin don gano musabbabin fashewar,” in ji shi.

Kafafen yaɗa labarai na cikin gida a kasar sun nuna bidiyon da ke nuna layin ’yan sanda da ke kewaye da makarantar, inda motoci masu ɗaukar marasa lafiya ke tsaye a gefe.

Sai dai hotunan masallacin ba su nuna wata mummunar lalacewa ba sakamakon harin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci
  • Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
  • Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga
  • Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato
  • Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Tabbatar Da Hannun Amurka Wajen Kaddamar Da Yaki Kanta
  • Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja
  • Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia
  • Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne